NYSC ta yi karin haske a kan bude sansanin horar da ma su hidimtawa kasa

NYSC ta yi karin haske a kan bude sansanin horar da ma su hidimtawa kasa

Hukumar kula da matasa ma su hidimar kasa (NYSC) ta ce ba zata bude sansanin horar da masu hidimar kasa ba sai gwamnatin tarayya ta bata izini.

A baya hukumar NYSC ta dakatar tare da bayar da umarnin rufe sansanin horar da masu hidimar kasa saboda dakile yaduwar kwayar cutar korona.

A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Adenike Adeyemi, ya fitar ranar Alhamis ya ce babu gaskiya a cikin labarin da ake yadawa a kan cewa NYSC za ta bude sansanin horo a 'yan kwamaki masu zuwa.

NYSC ta jaddada muhimmancin kare lafiyar ma'aikatanta tare da bayyana cewa ba zata bude kowanne sansani ba har sai ta tabbatar babu wata barazana dangane da yin hakan.

"Hukumar NYSC ta bawa kiyaye lafiyar ma'aikatanta da na matasa masu hidimar kasa fifiko, a saboda hakane muka dakatar da bayar da horo ga matasa masu hidimar kasa na rukunin 'B'.

NYSC ta yi karin haske a kan bude sansanin horar da ma su hidimtawa kasa
Matasa ma su hidimtawa kasa
Asali: UGC

"Duk da ko a yanzu haka mun gamsu cewa za a iya bude sansanin, NYSC ba zata bude sansanin bayar da horo ba sai gwamnatin tarayya ta bayar da izini.

DUBA WANNAN: Goyon bayan Giadom: Manyan APC hudu da ba zasu ji dadin shawarar da Buhari ya yanke ba

"Mu na shawartar ma su hidimar kasa da masu jiran shiga su nemi sahihan bayanai dangane da harkokin NYSC daga kafofinta na wasa labarai da ke dandalin sada zumunta da kuma sanarwar da take fitarwa a manyan jaridu na kasa," a cewar sanarwar.

Jawabin na hukumar NYSC na zuwa ne bayan wani kwamiti a karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayar da shawarar a dakatar da bude sansanin bayar da horo ga matasa ga masu hidimar kasa na tsawon shekara biyu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel