Mai Mala Buni ya fadi ta hanyar da zai warware rigingimun APC

Mai Mala Buni ya fadi ta hanyar da zai warware rigingimun APC

- APC ta gudanar da babban taron majalisar koli a gudanar da harkokin jam'iyyar (NEC) a ranar Alhamis

- Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayar da shawarar a rushe kwamitin gudanarwa na jam'iyyar APC (NWC) wanda Oshiomhole ya kafa

- An nada shugabancin rikon kwarya a karkashin jagorancin tsohon sakataren jam'iyya, gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni

Shugaban kwamitin rikon kwaryar shugabancin jam'iyyar APC, Mai Mala Buni, ya karbi ragamar tafiyar da harkokin jam'iyya tare da daukan alkawarin tabbatar da adalci ga dukkan mambobin APC.

Bayan kammala taron NEC a fadar shugaban kasa, sabon shugaban ya wuce kai tsaye zuwa hedikwatar jam'iyyar APC tare da sauran mambobin kwamitinsa 13.

Jami'an tsaron da suka garkame hedikwatar APC sun bude kofar shiga bayan zuwan Buni da tawagarsa jim kadan bayan kammala babban taron jam'iyya a Villa.

Da sanyin safiyar ranar Alhamis ne jami'an 'yan sanda suka rufe hedikwatar jam'iyyar APC tare da hana shugabannin jam'iyyar masu biyayya ga Oshiomhole shiga ofisoshinsu.

Da yake tattaunawa da manema labarai a hedikwatar APC, Buni, wanda shine gwamnan jihar Yobe, ya ce: "jam'iyya za ta yi tafiya da kowa da kowa, musamman jagororin APC.

"Dukkan mambobin jam'iyyar APC sun bayar da gudunmawa wajen gina jam'iyyar, a saboda haka za mu yi tafiya da kowa.

Mai Mala Buni ya fadi ta hanyar da zai warware rigingimun APC
Mai Mala Buni
Asali: Original

"Na san jam'iyyar APC sosai, saboda na taba rike mukamin babban sakataren jam'iyya har sau biyu, ina bawa dukkan mambobin jam'iyyar APC tabbacin samun adalci saboda tamkar 'yan uwan juna mu ke.

DUBA WANNAN: Goyon bayan Giadom: Manyan APC hudu da ba zasu ji dadin shawarar da Buhari ya yanke ba

"Ni dan cikin gida ne kuma na dawo ne domin warware rigingimun da jam'iyya ke fama da su, saboda idan ba mu warware wadannan matsaloli ba, matsalolin za su warware tubalin ginin jam'iyya.

"Babu wani kwamiti da ya ke da ikon da ya wuce na kwamtin NEC a cikin jam'iyya, a saboda haka babu mai ikon sauya hukuncin da NEC ta zartar."

Buni ya ce kwamitin NEC ya umarci dukkan mambobin APC su janye duk wata kara da suka shigar a gaban kotu dangane da rikicin da jam'iyya ke ciki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng