An samu mutane uku dauke da COVID-19 a gwamnatina Inji Makinde

An samu mutane uku dauke da COVID-19 a gwamnatina Inji Makinde

A jihar Oyo, mun samu labarin cewa gwaji ya tabbatar da cewa akwai masu dauke da cutar COVID-19 a cikin majalisar zartarwa ta gwamnatin Mai girma Seyi Makinde.

Injiniya Oluseyi Makinde ya bayyana haka da kansa a ranar Laraba, 24 ga watan Yuni, 2020.

Gwamnan ya bayyana wannan ne a wani jawabi da ya fitar a shafinsa na Twitter a jiya.

Ga jawabin na sa:

“A yau mu ka samu sakamakon gwajin cutar COVID-19 na duka ‘yan majalisar gwamnan jihar Oyo. Abin takaici, sakamakon gwajin sun nuna mutane uku sun kamu da COVID-19”

Makinde ya kara da cewa:

“An kuma samu mutum biyu da sakamakon gwajinsu bai kammala ba, saboda haka za a sake yi masu gwajin.” — Seyi Makinde (@seyiamakinde).

A jihar Oyo kawo yanzu, akwai mutane 1,055 da wannan cuta ta harba. Kafin mukarraban gwamnan, shi kan sa Mai girma Seyi Makinde ya yi jinyar COVID-19 na mako guda.

KU KARANTA: Mutane 640 aka samu dauke da kwayar COVID-19 a Ranar Laraba

An samu mutanen da ke dauke da COVID-19 a gwamnatina Inji Makinde
Seyi Makinde Hoto: Twitter/Seyiamakinde
Asali: Twitter

Makinde ya shaida cewa an rufe ofisoshin wadannan manyan gwamnati da su ka kamu da cutar, kuma an fara kokarin tuntubar wadanda su ka samu alaka da su domin dauke su daga jama’a.

Gwamnan ya gargadi mutanen jihar Oyo cewa: “Ina kara maimaita cewa COVID-19 ta na nan sosai tare da mu. Don mu na daukar matakan bude kasuwanni, ba ya nufin cutar ta bace.”

Injiniya Makinde ya kara da jan-kunne: “Dole mu dauki matakan kare kanmu da iyalanmu.”

A cewarsa dole a dauki matakan rigakafin kare kai daga wannan cuta ta hanyar wanke hannuwa da rufe fuskoki tare da gujewa cinkoso da bada tazara wurin shiga cikin taron jama’a.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel