APC: Bayan samun goyon bayan Buhari, Giadom ya bayyana wata damuwarsa

APC: Bayan samun goyon bayan Buhari, Giadom ya bayyana wata damuwarsa

Shugaban riko na jam'iyyar APC, Victor Giadom, ya ce ya damu a kan halayyar wasu mambobin jam'iyyar da suka ki mika wuya ga matakin babban kwamitin koli na gudanarwa a APC (NEC).

Giadom ya kira babban taron masu ruwa da tsaki a harkokin gudanar da jam'iyyar APC (NEC) kuma har shugaba Buhari ya nuna niyyarsa ta halartar taron, wanda za a yi ranar Alhamis a fadar shugaban kasa.

Kwamitin gudanar da ayyuka na jam'iyyar APC na bangaren Abiola Ajimobi, ya yi watsi da gayyatar da aka yi musu na taron shugabannin jam'iyyar.

Bayan taron da kwamitin ya gudanar na sa'o'i masu tarin yawa, NWC ta kara da cewa an hurewa shugaban kasa Muhammadu Buhari kunne kafin ya amince da taron da shugabancin riko a karkashin Giadom.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa, sakamakon tsanantar rikicin cikin gida a jam'iyyar APC, bangaren Victor Giadom ya kira taron shugabannin jam'iyyar na gaggawa a ranar Alhamis.

Da yake magana yayin wani shirin gidan talabijin na 'Channels', Giadom ya ce babban makasudin kiran taron shine domin tattauna matsalar shugabanci da jam'iyyar ta fada.

APC: Bayan samun goyon bayan Buhari, Giadom ya bayyana wata damuwarsa
Victor Giadom
Asali: UGC

"Ba ina ne magana ne da yawun fadar shugaban kasa ba, amma mu na sa ran shugaban kasa zai halarci wurin taron a matsayinsa na babban shugaba a jam'iyyar APC," a cewar Giadom.

DUBA WANNAN: Sanatan APC daga arewa ya amince zai karbi belin Maina

Sannan ya cigaba da cewa; "abu na farko shine mu duba batun rigingimun da jam'iyya ke ciki domin neman mafita. Na riga na bayyana kaina, na sanar cewa kwamitin gudanarwa na yanzu ba zai iya warware matsalar da jam'iyya ke ciki ba.

"Akwai bukatar babban kwamitin koli na gudanarwa (NEC) ya shiga cikin lamarin domin kawo gyara.

"Amma na shiga damuwa a kan halayyar da wasu daga cikin abokaina suka nuna ta kin karrama gayyatar halartar taron NEC.

"Ina shawartarsu su yi amfani da bayanan gayyata da aka aika mu su domi halartar taron NEC da za a yi a kan manhajar 'zoom' ta hanyar amfani da fasahar yanar gizo kamar yadda aka tsaro."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng