Goyon bayan Giadom: Manyan APC hudu da ba zasu ji dadin shawarar da Buhari ya yanke ba
Garba Shehu, kakakin shugaban kasa, ya sanar da cewa shugaba Buhari ya goyi bayan Giadom a matsayin halastaccen shugaban jam'iyyar APC na rikon kwarya.
Jam'iyyar APC ta fada cikin rigingimun shugabanci bayan wata kotun daukaka kara ta tabbatar da dakatar da Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam'iyyar APC na kasa.
Duk da kwamitin gudanarwa (NWC) na jam'iyyar APC ya sanar da sunan Abiola Ajimobi a matsayin shugaban rikon kwarya, Giadom ya yi gaban kansa wajen sanar da cewa shine halastaccen shugaban jam'iyya na rikon kwarya.
Mambobin NWC na APC sun yi watsi da Giadom tare da sanar da sunan Eta Hilliard a matsayin shugaban da zai jagoranci jam'iyyar saboda Ajimobi bashi da lafiya.
Aminceware da Buhari ya yi da shugabancin Giadom tamkar 'yar manuniyace a kan rashin karfin gwuiwar da yake da shi a kan kwamitin NWC da shugabancin Oshiomhole ya kafa.
Ma su fashin bakin siyasa sun bayyana cewa shawarar da Buhari ya yanke ta goyawa Giadom baya ba zata yi wa jagoran jam'iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, dadi ba.
Kazalika, shugaban jam'iyyar APC da aka dakatar, Adams Oshiomhole, ba zai ji dadin shawarar da Buhari ya yanke ba, musamman idan aka duba yadda Giadom ya so ya warware hukuncin korar takarar gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki.
Ragowar manyan 'ya'yan APC da matakin da shugaba Buhari ya dauka zai sosawa rai sun hada da Abiola Ajimobi, mutumin da NWC ta amince ya rike jam'iyyar na rikon kwarya, da kuma Hilliard Eta, mutumin da NWC ta yarda ya wakilci Ajimobi kafin ya warke.
DUBA WANNAN: Sanatan APC daga arewa ya amince zai karbi belin Maina
Mambobin NWC na APC sun yi watsi da Giadom tare da sanar da sunan Eta Hilliard a matsayin shugaban da zai jagoranci jam'iyyar saboda Ajimobi bashi da lafiya.
A cewar Garba Shehu, shugaba Buhari zai halarci taron masu ruwa da tsaki a gudanar da harkokin APC a karkashin jagorancin Giadom.
APC za ta yi babban taro ranar Alhamis, 25 ga watan Yuni, a fadar shugaban kasa da ke Abuja domin warware rigingimun kabilanci da APC ta fada ciki tun bayan tabbatar da dakatar da shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng