Zaben Edo: Ban janye wa Obaseki ba - Dan takarar PDP

Zaben Edo: Ban janye wa Obaseki ba - Dan takarar PDP

Kenneth Imansuagbon, dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben Satumba da za a yi a jihar Edo, ya karyata rade-radin cewa ya karbi kudi don janyewa.

An dai yi zargin cewa Imansuangbon ya karbi dala miliyan biyu daga hannun Gwamna Godwin Obaseki domin ya janye masa gabannin zaben fidda gwanin da jam’iyyar za ta yi a gobe domin tsayar da gwaninta.

Imansuangbon, wanda ya kasance lauya da aka fi sani da suna ‘Rice Man’, ya bayyana a wani jawabi cewa sabanin rade-radin da ake yi har yanzu yana takarar gwamnan sannan cewa bai janye wa Obaseki ba.

Ya ci gaba da cewa ya shiga tseren gwamnan ne don yin nasara ba wai ya kasance cikin kidayar masu neman tikitin PDP ba, jaridar The Sun ta ruwaito.

Zaben Edo: Ban janye wa Obaseki ba - Babban dan takarar PDP
Zaben Edo: Ban janye wa Obaseki ba - Babban dan takarar PDP Hoto: The Sun
Asali: UGC

Ya kara da cewar tawagar gwamnan ne ke yada jita-jitan cewa shi ya karbi dala miliyan biyu daga hannunsa domin yi masa fashin kuri’unsa a wajen wakilan jam’iyyar.

“Gwamnan ya san cewa na shahara da wakilai kuma yana yin duk iya kokarinsa wajen ganin ya chanja hakan.

“Ban karbi kudi ba kuma bana niyan karban kowani kudi don janyewa daga tseren neman tikitin PDP.

“Na kuma fahimci cewa suna kokarin sauya jerin wakilai don kansu. Ina son yin gargadin cewa idan suka yi kokarin haka, za mu yi duk wacce za mu yi don hana hakan kuma za mu hadu a kotun shari’a,” in ji shi.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Buhari ya shiga taron FEC ta yanar gizo

Imansuangbon ya bukaci wakiltan jam’iyyar da su fito su zabe shi a zaben fidda gwani, inda ya yi alkawarin kawo karshen talauci a jihar Idan aka zabe shi a matsayin gwamna.

A wani labarin kuma, mun ji cewa gabannin zaben fidda dan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Edo wanda za a yi a ranar Juma’a, babban dan takarar jam’iyyar da ke kan gaba, Mista Gideon Ikhine, ya janye wa Gwamna Godwin Obaseki.

Ikhine ya sanar da shawararsa na janye wa gwamnan a ranar Litinin, 22 ga watan Yuni a wani taro a Benin.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa Gwamna Obaseki, shugaban jam’iyyar na jihar, Dr Tony Aziegbemi da sauran shugabannin jam’iyyar a fadin jihar sun hallara a wajen taron.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel