Ban san komai a rigimar APC ba, ya kamata a bar doka ta yi aiki inji Amaechi

Ban san komai a rigimar APC ba, ya kamata a bar doka ta yi aiki inji Amaechi

- Jam’iyyar APC ta na fama da tarin rikici iri-iri na cikin gida a halin yanzu

- Daga cikin inda wannan rigima ta cabe akwai Ribas inda Amaechi ya fito

- Rotimi Amaechi ya ce babu wadanda ya ke marawa baya a wannan rikici

Yayin da rigima ke barkowa jam’iyyar APC mai mulki, Rotimi Amaechi ya nuna cewa sam babu ruwansa da rikicin da ake ta faman yi, ya ce abin da ya ke so shi ne a bar doka ta yi aikinta.

Ministan sufurin Najeriya, Rt. Hon. Rotimi Amaechi ya fito ya yi magana game da rikicin da ake yi, ya ce bai da wata masaniya a game da abin da ke ta faruwa kamar yadda ake ta rade-radi.

A lokacin da aka yi hira da Ministan a gidan talabijin a ranar Talata, 23 ga watan Yuni, ya ce dole a bi abin da doka a ko yaushe. Ya ce ba ya son cusa kansa a cikin harkar siyasar Najeriya.

“Ni ban san abin da ke faruwa a APC a Ribas ba. Ban sani ba. Abin da na yi shi ne kauracewa sha’anin siyasa, ko da ina damuwa a cikin rai na; babu yaro a cikin (APC), dukkanmu manya ne.”

KU KARANTA: ‘Ya ‘yan Jam’iyyar APC sun kawo mana koke-koke 170 – Kwamitin sulhu

Ban san komai a rigimar APC ba, ya kamata a bar doka ta yi aiki inji Amaechi
Tsohon Gwamnan Ribas Rotimi Amaechi
Asali: Twitter

“Mutanen Najeriya sun san ni da fadar gaskiya da gar-da-gar. Wasu su na yi wa wannan kallon girman-kai, ko kwaratsi, ko ma menene. Menene zan fada da ban fada a da ba?" Inji Amechi.

Amaechi ya kara da cewa: “Siyasar cikin gida, da gwagwarmayar jam’iyya ce. Saboda haka na fada sau da-dama tun lokacin da mu ka yi yaki a 2015, kasar nan ba za ta cigaba da tafiya a haka ba.”

Ministan ya ce ba wai bai da ikon yin wani abu ba ne, sai dai zai tsaya a gefe ya na lura da komai. Amaechi ya bada shawara ga magoya bayansa da su guji tada rikici, su rika tafiya gaban kotu.

Ya ce: “Na yi imani duk yadda ka ke fushi, da yadda ake juya hukumomin gwamnati, shiyasa wani Alkali ya fada mani ‘Ina da damar yin kuskure, shiyasa za daukaka kara har kotun koli.”

“’Ya ‘yana da ‘yanuwana sun san cewa ni ba mutum ba ne wanda zai saba doka. Saboda haka ba zan zo in taimaka maku ba, idan kai ‘danuwana ne ko ‘dana ka dauki doka a hannunka.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel