Yanzu-yanzu: Buhari ya shiga taron FEC ta yanar gizo

Yanzu-yanzu: Buhari ya shiga taron FEC ta yanar gizo

- Shugaba Muhammadu Buhari yana shugabantar taron majalisar zartarwa a fadar shugaban kasa da ke Abuja ta yanar gizo

- An fara taron da karfe 10 na safiyar yau Laraba, 24 ga watan Yuni

- Taron ya samu halartan mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo da manyan jami'an gwamnati

Shugaba Muhammadu Buhari yana jagorantar taron majalisar zartarwa ta tarayya a gidan gwamnati da ke Abuja ta yanar gizo.

An fara taron da karfe 10 na safe sannan ya samu halartar ministoci tara da wasu manyan jami'an gwamnati.

Daga cikin wadanda suka samu halarta akwai mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo; sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha; shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.

Yanzu-yanzu: Buhari ya shiga taron FEC ta yanar gizo
Yanzu-yanzu: Buhari ya shiga taron FEC ta yanar gizo Hoto: Buhari Sallau
Asali: Twitter

Har ila yau a taron harda mai bada shawara na musamman a kan tsaron kasa, Janar Babagana Monguno.

Ministocin da suka samu halartar taron sun hada da Ministar kudi, kasafi da tsari, Zainab Ahmed; ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola; Antoni janar kuma ministan shari'a, Abubakar Malami.

KU KARANTA KUMA: Dalilan da suka sa na tsaya wa Maina - Sanata Ndume

Ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika da kuma ministan wasanni da matasa, Sunday Dare; ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed,.

Sauran sun hada da ministar harkokin mata, Dame Pauline Fallen; minisitan ruwa, Injiniya Suleiman Adamu; karamin ministan man fetur Timipre Sylva da karamin ministan kasafi, kudi da tsari, Clement Agba.

Kamar yadda hadimin Shugaban kasar, Buhari Sallau ya wallafa hotunan taron a shafinsa na Twitter ya ce: “Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagorani taron majalisar FEC ta yanar gizo.

"Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Farfesa Osinbajo da sakataren tarayya Mista Boss Mustapha a lokacin taron majalisar zartarwa na yanar gizo da aka gudanar a zauren fadar shugaban kasa."

A wani labari na daban, tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung, ya kushe gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan rashin tsaron da ya addabi yankin arewa.

Ya bayyana gwamnatin a matsayin mafi munin gwamnati da aka taba yi a tarihin kasar nan.

A yayin jawabinsa a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Dalung ya ce duk da makuden kudin da ake warewa tsaro, babu abinda ya sauya a kan kashe rayukan 'yan Najeriya tamkar dabbobi.

Ya zargi hadiman shugaban kasar da kin sanar da shi gaskiya a yayin yaki da ta'addanci da kuma 'yan bindiga.

Ya ce Buhari ya ja kunnen 'ya'yansa da ke aiki a karkashinsa wadanda basu sanar da shi gaskiya a kan al'amarin tsaro a kasar nan. Ya bukacesu da su daina zagin shugabannin arewa wadanda ke fadin gaskiya.

Ya kushe abinda ya bayyana da halin ko in kula na shugaban kasar da yake fitar da makuden kudin Najeriya don kashewa a kan tsaro amma babu wani sauyi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel