Annobar COVID-19 ta hana Majalisar APC zama domin sauraron korafi

Annobar COVID-19 ta hana Majalisar APC zama domin sauraron korafi

Mun samu labari daga jaridar Punch cewa an kai wa shugabannin jam’iyyar APC korafi akalla 170. Kwamitin sulhu na kasa ne ya ke karbar wannan koke-koke daga jihohin Najeriya.

Sakataren kwamitin, Sanata John Enoh ya bayyana wannan a lokacin da ya yi hira da jaridar Punch a ranar Litinin, 22 ga watan Yuni, 2020. Ya ce korafin da ke gabansu ya karu a yanzu.

Da ya ke magana game da abin da ya hana kwamitin zama, John Enoh ya ce haramta zirga-zirga da gwamnati ta yi domin dakile yaduwar cutar COVID-19 ya sa su ka dakatar da taronsu.

Sanata Enoh ya yi wannan bayani ne a lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin jihohin APC su ke kokarin ganin sun dinke barakar da ta bijirowa jam’iyyar.

A lokacin da Muhammadu Buhari da gwamnoni su ke taro a fadar shugaban kasa, sai aka fahimci cewa har yanzu ba a kama hanyar shawo kan matsalolin cikin gidan da ake fama da su ba.

A jiya ne Victor Giadom ya aikawa manyan Jam’iyya goron gayyatar taron NEC. Giadom ya yi shelar taron NEC bayan kotu ta dakatar da shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole.

A bana ne aka nada Cif Bisi Akande domin ya jagoranci kwamitin sulhun na jam’iyyar APC. Hakan na zuwa ne bayan sauran kwamitocin da aka kafa sun gaza sasanta rikicin gidan.

KU KARANTA: Giadom ya kira taron Jam’iyya, ya ce Buhari ya san da maganar

Annobar COVID-19 ta hana Majalisar APC zama domin sauraron korafi
Shugaban kwamitin sauraron korafi a APC da Buhari
Asali: UGC

A shekarar bara, Adams Oshiomhole ya bukaci Ahmad Lawan ya sasanta rigingimun da ake yi tsakanin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC. Irinsu gwamnan Edo ne su ka jawo rushewar kwamitin.

Yanzu APC ta na fama da rigingimu iri-iri a jihohin Edo, Zamfara, Bayelsa, Ribas da Ondo. A Edo lamarin ya yi kamari har ta kai gwamnan jihar ya koma PDP bayan hana sa neman takara.

A jihar Zamfara, rikicin cikin gida ya ci jam’iyyar APC har PDP ta lashe duka kujerun jihar a zaben 2019. A Ondo kuma gwamnan jihar ya samu sabani da wani bangare na jam’iyyar APC.

A cewar Enoh, saboda yanayin aikin da ke gabansu, sun gaza shirya taro ta yanar gizo domin kwamitin ya fara dinke barakar da su ke fama da ita, saboda manyan tituna da ke rufe.

“Shugabanmu Cif Bisi Akande ya makale a jihar Osun, mu na sa ran cewa daga an bude filayen jirgi, ko da babu tabbacin yashe za a koma aiki, daga nan sai mu ga yadda za a fara zama.”

“Ana samun karin korafi bayan lokacin da mu ka zauna, amma ba masu yawa ba. Mun samu koke-koke kusan 170 daga ‘yan jam’iyya. An ware mana aikin da za mu yi.” Inji Enoh.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel