Ba mu ce a bude makarantu ba tukuna – Inji Gwamnatin Kano

Ba mu ce a bude makarantu ba tukuna – Inji Gwamnatin Kano

Gwamnatin jihar Kano ta yi watsi da rahotannin da ake ji na cewa ta na tunanin bude makarantun da ke jihar.

Ana rade-radin gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta kafa wani kwamiti da zai duba yadda za a dawo koyarwa a makarantun da yanzu su ke rufe a sanadiyyar annobar cutar COVID-19.

Ma’aikatar ilmi ta jihar ta ce wannan rahoto ba gaskiya ba ne. Sakataren yada labarai na ma’aikatar, Malam Aliyu Yusuf ya ce wadannan rahotanni ‘labaran bogi’ ne marasa tushe.

A cewarsa rahoton ya sha ban-ban da ainihin halin da ake ciki a jihar Kano.

“Kano kamar sauran jihohi ta samu takarda daga ma’aikatar ilmin gwamnatin tarayya a game da sharudan da za a bi wajen bude makarantu a lokacin da ya dace, inda mu ka bada gudumuwarmu.”

Malam Aliyu Yusuf ya kuma kara da cewa: “A wajen bada gudumuwa ne mu ka kafa kwamiti da zai yi wannan aiki, ya kuma tuntubi gwamnatin tarayya.”

KU KARANTA: Ganduje ya kara bada damar sararawa a Jihar Kano

Ba mu ce a bude makarantu ba tukuna – Inji Gwamnatin Kano
Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Facebook

A cewar sakataren yada labaran, gwamnati ba ta haramta duk wani karatu da ake yi wa ‘yan makaranta ta kafafen yanar gizo ba. Makarantun kudi ne ake samu su na yin wannan.

Ya ce: “Ma’aikatar ilmi ta na kuma watsi da rade-radin da ke yawo na cewa an bada umarni a dakatar da makarantun ‘yan kasuwa daga dakatar da koyawa ‘dalibansu karatu ta yanar gizo.”

“Shi ma wannan labari ba gaskiya bane, ita ma gwamnati ta na yin irin wannan shirye-shirye ta gidajen rediyo da talabijin ga ‘daliban makarantunta.” Inji ma’aikatar ilmin jihar.

Jami’in gwamnatin ya ce amma an hana makarantun ‘yan kasuwa gudanar da jarrabawa da gwaji ta kafafen yada labarai. Hukumar dillacin labarai na kasa ta fitar da wannan rahoto.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel