COVID-19: Majalisar jihar Kaduna ta bada umarnin gwajin dole ga dukkan mambobinta

COVID-19: Majalisar jihar Kaduna ta bada umarnin gwajin dole ga dukkan mambobinta

- Majalisar dokokin jihar Kaduna ta umurci dukkanin ma'aikata da mambobinta da su je su yi gwajin korona

- Kakakin majalisar jihar Kaduna, Alhaji Yusuf Zailani ne ya bayar da wannan umurni

- Ya ce hakan ya zama dole bayan wani ma'aikacin majalisar ya kamu da cutar

Kakakin majalisar jihar Kaduna, Alhaji Yusuf Zailani ya umarci dukkan ma'aikatan majalisar da masu wakilci da su mika kansu don gwajin cutar coronavirus.

Ya sanar da hakan ga manema labarai ta bakin mataimakin shugaban kwamitin lafiya na majalisar, Ali Kalat, a ranar Talata a garin Kaduna.

COVID-19: Majalisar jihar Kaduna ta bada umarnin gwajin dole ga dukkan mambobinta
COVID-19: Majalisar jihar Kaduna ta bada umarnin gwajin dole ga dukkan mambobinta Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Kalat ya ce wannan umarnin ya zama dole bayan wani ma'aikacin majalisar ya kamu da cutar. Ya ce babu dan majalisar da ya kamu amma.

"Amma ya zama dole mu mika kanmu don gwaji don tabbatar da ingancin lafiyar dukkan 'yan majalisar.

"Kakakin majalisar ya bada wannan umarnin na cewa kowanne ma'aikaci ya garzaya gwaji," yace.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Matsala ya kunno kai a PDP yayinda Wike ya zame daga lamarin zaben gwamnan Edo

Kalat ya ce, "Bayan kammala gwajin, za mu rufe majalisa tare da sauraron umarni na gaba."

A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto a baya cewa gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce bayan sassauta dokar kulle da yayi a jihar Kaduna, mataki na gaba shine kiyaye yaduwar annobar korona wacce take hannun mutane.

El-Rufai ya roki jama'ar jihar da su dauka dawainiyar yaki da yaduwar cutaf korona. Ya ce kada a mayar da kokarin da yayi a baya ta hanyar kin kiyaye dokokin hana yaduwar cutar.

Gwamnan wanda ya mika wannan rokon a ranar Talata, ya mika sakon godiyarsa ga jama'ar jihad Kaduna a kan yadda suka yi hakurin watanni biyu da rabi wurin dakile annobar.

"Mu mutunta sadaukarwar da muka yi ta hanyar tallafawa kanmu tare da dakile yaduwar muguwar cutar. Kun yi babban kokari ta yadda kuka zauna a gida na makonni goma. Mu nuna cewa za mu iya zama lafiya duk da sassauta dokar da aka yi," ya kara da cewa.

El-Rufai ya yi kira ga dattawan da suka wuce shekaru 50 da su zauna a gida duk da sassauta dokar hana walwalar da aka yi a jihar Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel