Yanzu Yanzu: Matsala ya kunno kai a PDP yayinda Wike ya zame daga lamarin zaben gwamnan Edo

Yanzu Yanzu: Matsala ya kunno kai a PDP yayinda Wike ya zame daga lamarin zaben gwamnan Edo

- Gwamna Nyesome Wike ya zame daga taron sulhu na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Edo

- Wike ya zargi wasu mambobin kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar na kasa da daukar nauyin wasu wallafe-wallafe domin zubar masa da kima

- Gwamnan na jihar Rivers ya gargadi kwamitin a kan yin abunda zai lalata jam'iyyar

Gwamnan jihar Rivers, Nyesome Wike ya janye daga taron sulhu na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Edo.

Wike ya zargi wasu mambobin kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar na kasa da daukar nauyin wasu wallafe-wallafe domin zubar masa da martabarsa.

Gwamnan na jihar Rivers ya gargadi kwamitin daga yin duk wani abu da zai lalata jam’iyyar, AIT Live ta ruwaito.

Yanzu Yanzu: Matsala ya kunno kai a PDP yayinda Wike ya zame daga lamarin zaben gwamnan Edo
Yanzu Yanzu: Matsala ya kunno kai a PDP yayinda Wike ya zame daga lamarin zaben gwamnan Edo Hoto: AIT
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Rikicin APC: Kotu ta haramtawa Victor Giadom alakanta kansa da jam'iyyar APC

A gefe guda, mun ji cewa gabannin zaben fidda dan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Edo wanda za a yi a ranar Juma’a, babban dan takarar jam’iyyar da ke kan gaba, Mista Gideon Ikhine, ya janye wa Gwamna Godwin Obaseki.

Ikhine ya sanar da shawararsa na janye wa gwamnan a ranar Litinin, 22 ga watan Yuni a wani taro a Benin.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa Gwamna Obaseki, shugaban jam’iyyar na jihar, Dr Tony Aziegbemi da sauran shugabannin jam’iyyar a fadin jihar sun hallara a wajen taron.

Da yake sanar da hukuncin nasa, dan takarar ya bayyana cewa babu nasara ba tare da sadaukarwa ba, inda ya kara da cewar sauya shekar gwamnan zuwa jam’iyyar addu’a ne da Allah ya amsawa jam’iyyar da takararsa.

Ya bayyana cewa mutane biyu na iya kasancewa da hange iri guda amma yadda za su tunkare su zai bambanta.

khine ya kara da cewa ba wai zai ja baya bane, illa zai kasance a bayan mutumin da zai jagoranci jam’iyyar zuwa ga tafarkin nasara a ranar 19 ga watan Satumba.

Ya ce da shi da magoya bayansa sun yanke shawarar aiki tare da gwamnan domin tabbatar da inganci a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel