An kama wani matashi ya na lalata da alade
An gurfanar da Ayokunbi Olaniyi, wani matashi mai shekaru 22, a gaban wata kotun majistare da ke yankin Iyaganku a garin Ibadan, jihar Oyo, bisa zarginsa da saduwa da alade.
Rundunar 'yan sanda ta na tuhumar Olaniyi, mazaunin yankin Eleti - Odo a kan titin Iwo a garin Ibadan, bisa tuhumarsa da aikata laifi guda daya; laifin saduwa da alade, wanda hakan ya sabawa dokar rayuwa ta hankali.
Dan sanda mai gabatar da kara, Insifekta Opeyemi Olagunju, ya sanar da kotu cewa an kama Olaniyi ya na saduwa da alade a yankin unguwar Elewi - Odo, Ibadan, da misalin karfe 4:00 na yammacin ranar 2 ga watan Afrilu.
Dan sandan ya bayyana cewa Olaniyi ya na aiki da gidan gonar uwargida Adenike Taiwo wanda ke yankin Elewi - Odo a garin Ibadan.

Asali: Twitter
Ya sanar da kotu cewa laifin matashin ya sabawa sashe na 214 (2) na kundin laifuka da hukunce - hukunce wanda aka kirkira a jihar Oyo a shekarar 2000.
DUBA WANNAN: Dalilin da yasa 'yan N-Power 12,000 basu samu alawus na wata uku ba - Minista
Matashin ya amsa laifin da ake tuhumarsa da aikatawa.
Mumin Jimoh, lauya mai kare wanda ake tuhuma, ya roki kotun ta kasance mai sassauci a hukuncin da za ta zartar a kan Olaniyi.
Lauya Jimoh ya shaidawa kotun cewa mai gonar ta yafewa matashin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng