COVID-19: Bafarawa ya yi muhimmin kira ga ma'aikatan gwamnati

COVID-19: Bafarawa ya yi muhimmin kira ga ma'aikatan gwamnati

- Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Dalharatu Bafarawa ya yi kira ga ma'aikatan gwamnati a Najeriya da su sadaukar da wani kaso a albashinsu ga gwamnati saboda korona

- Bafarawa ya bukaci ma'aikatan da su yi amfani da kason wajen siya wa 'yan Najeriya marasa karfi abinci

- Jigon na PDP ya shawarci gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi da su nemo hanyar samar da kudin shiga don rage radadin kullen da 'yan Najeriya ke fuskanta

Sakamakon annobar korona, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Dalharatu Bafarawa ya yi kira ga ma'aikatan gwamnati a Najeriya da su sadaukar da wani kaso a albashinsu don bai wa gwamnatocin tarayya da na jiha damar tallafi ga 'yan Najeriya da basu aiki.

Tsohon gwamnan yayin magana a kan yadda annobar korona ta zama ruwan dare a duniya, ya ce ta tada hankulan jama'a a fadin duniya.

Bafarawa wanda ya yi jawabin ga manema labarai a Sokoto, ya kara da shawartar gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi da su nemo hanyar samar da kudin shiga don rage radadin kullen da 'yan Najeriya ke fuskanta.

COVID-19: Bafarawa ya yi muhimmin kira ga ma'aikatan gwamnati
COVID-19: Bafarawa ya yi muhimmin kira ga ma'aikatan gwamnati Hoto: Leadership
Asali: Depositphotos

"Alama na nuna cewa babu kasar da annobar ta tsallake da muguwar illarta. Sannan kuma alamu na nuna babu lokacin tafiyarta takamaimai," yace.

Tsohon gwamnan kuma jigo a jam'iyyar PDP ya yi kira ga ma'aikatan gwamnati da su dage wurin amfanar da sauran jama'a.

Ya bada shawarar cewa su sadaukar da wani kaso na albashinsu don siya wa 'yan Najeriya marasa karfi abinci.

KU KARANTA KUMA: Edo 2020: Babban dan takarar PDP ya janye wa Gwamna Obaseki

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa a yayin nuna damuwa game da annobar, Bafarawa ya ce "alamu na nuna cewa babu kasar da ba zata koka da wannan annobar ba.

"A wasu kasashen duniya kamar su China, Italy, Spain da Amurka, rashin rayukan da ake yi yayi yawa. Dubban mutane ke mutuwa a kowacce rana. Hakazalika ba a tunanin ranar tafiyar annobar," yace.

A wani labarin kuma, mun ji cewa tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, wanda yanzu shine shugaban kwamitin kula da sojin kasar nan, Sanata Ali Ndume, ya bayyana cewa 'yan majalisar tarayya da masu manyan mukamai a kasar nan ne ke morar albashi mai tarin yawa.

Sai dai kuma ya ce talakawan Najeriya ke cikin wani hali, jaridar Punch ta ruwaito.

Ya ce mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Muhammadu Sanusi sun yi gaskiya a kan yadda ake tafiyar da gwamnatin Najeriya cike da tsada wanda yace ba dole bane hakan ya ci gaba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel