Manyan Arewa sun sha ban-ban da Ministan shari’a a kan binciken Ibrahim Magu

Manyan Arewa sun sha ban-ban da Ministan shari’a a kan binciken Ibrahim Magu

A jiya Litinin, 22 ga watan Yuni, manyan masu magana da babbar murya a Arewacin Najeriya su ka fara bayyana ra’ayinsu game da korafin da Ministan shari’a ya yi a kan shugaban EFCC.

Abubakar Malami SAN ya rubuta wata takarda, inda ya nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauke Ibrahim Magu daga kujerar EFCC saboda zargin badakala da wasu laifuffuka da-dama.

Wasu daga cikin manyan Arewa da ke Kaduna da Kano sun yi magana da jaridar Vanguard, su na zargin Abubakar Malami da yunkurin ganin bayan Ibrahim Magu duk da kokarin da ya ke yi.

Wadanda su ka yi magana sun hada da tsohon ‘dan siyasa, Dr. Junaid Mohammed, jagoran hamayya a Kaduna, Danjuma Sarki da kuma wani shugaban kungiyar CAN, Rabaren John Joseph Hayab.

Dr. Junaid Mohammed ya yi kaca-kaca da Ministan shari’a na kokarin zargin Magu da sata, rashin biyayya da sabawa doka, ya ce Malami ya yi wannan ne saboda ya gaza juya wuyan Magu.

A dalilin haka Junaid Mohammed ya ba Ministan shawara ya yi murabus, sannan ya fito ya nemi afuwar ‘yan Najeriya da shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya ke neman ci wa mutunci.

KU KARANTA: Buhari ya bada goyon bayan a binciki zargin da ke kan wuyan Magu

Manyan Arewa sun sha ban-ban da Ministan shari’a a kan binciken Ibrahim Magu
Mukaddashin Shugaban EFCC Ibrahim Magu Hoto: EFCC
Asali: Depositphotos

“Malami ya yi maza ya yi murabus idan ba ya jin dadin aiki da Magu, mutumin da ake yabo kuma marasa gaskiya su ke tsoro saboda irin namijin jajircewarsa wajen yaki da rashin gaskiya.”

Ya ce: “Hakan na nufin Magu ya sabawa dokar kasa, ya kyale AGF ya rika cin karensa babu babbaka, ba tare da la’akari da dokokin kasa ba.” Mohammed ya ce Ministan ya ajiye aikinsa.

A cewar Dattijon, Ministan ya na kokarin cin mutuncin shugaban kasa ne, kuma ya bada shawarar ayi ta-ka-tsan-tsan da bincike a kan zargin da Ministan ya ke yi wa shugaban EFCC.

Danjuma Sarki wanda jigon PDP ne a jihar Kaduna, ya na ganin cewa takardar da ta fito daga Ministan, ta fallasa irin satar da ake tafkawa ne a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Shi kuma shugaban CAN na Kaduna, John Joseph Hayab ya yi tir da AGF na fitowa fili ya yi magana, ya ce kamata ya yi ace Ministan ya kira shugaban na EFCC su tattauna cikin mutunci.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel