Damfarar da sunan matar marigayi Abba Kyari: Rundunar 'yan sanda ta kama Aminu Ado
Rundunar 'yan sanda ta kama wani mutum, Mallam Aminu Ado, mai shekaru 58, wanda ke sojan gona ta hanyar gabatar da kansa a matsayin matar marigayi Abba Kyari domin ya damfari jama'a.
Kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, DCP Frank Mba, ya gabatar da mai laifin a gaban manema labarai a ranar Litinin.
Mba ya bayyana cewa an fi sanin mutumin da 'Al Amin Yerima', kuma da ma tsohon mai laifi ne da ya kware wajen shirya salo salon damfara.
A cewar Mba, Yerima ya na tuntubar manyan mutane a wayar salula da sunan matar marigayi Abba Kyari tare da neman tallafi da gudunmawa domin shiryawa marigayin addu'o'i na musamman.
"Daga cikin irin manyan mutanen da ya ke tuntuba ne wasu suka yi zargin da wata manufa, lamarin da yasa suka sanar da rundunar 'yan sanda.
"Shekarunsa 58, ya na bamu hadin kai a binciken da muke gudanarwa. Hukumar EFCC ta taba gurfanar da shi a shekarar 2019 a gaban wata babbar kotun tarayya har aka yanke masa hukuncin daurin wata uku a gidan yari," a cewar Mba.
DUBA WANNAN: Sanata Usman Kadiri ya lissafa mutane biyu da ke barazanar rusa APC
Kakakin rundunar 'yan sandar ya ce Yerima ya na da wata manhaja a kan wayarsa da ke sauya muryar namiji zuwa muryar mace wacce yake amfani da ita domin damfarar mutane.
Sai dai, mai laifin ya ce shi makusanci ne ga iyalin marigayi Abba Kyari kuma ya na kokarin shirya masa taron addu'o'i na musamman ne.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng