Edo 2020: Babban dan takarar PDP ya janye wa Gwamna Obaseki

Edo 2020: Babban dan takarar PDP ya janye wa Gwamna Obaseki

Gabannin zaben fidda dan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Edo wanda za a yi a ranar Juma’a, babban dan takarar jam’iyyar da ke kan gaba, Mista Gideon Ikhine, ya janye wa Gwamna Godwin Obaseki.

Ikhine ya sanar da shawararsa na janye wa gwamnan a ranar Litinin, 22 ga watan Yuni a wani taro a Benin.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa Gwamna Obaseki, shugaban jam’iyyar na jihar, Dr Tony Aziegbemi da sauran shugabannin jam’iyyar a fadin jihar sun hallara a wajen taron.

Da yake sanar da hukuncin nasa, dan takarar ya bayyana cewa babu nasara ba tare da sadaukarwa ba, inda ya kara da cewar sauya shekar gwamnan zuwa jam’iyyar addu’a ne da Allah ya amsawa jam’iyyar da takararsa.

Ya bayyana cewa mutane biyu na iya kasancewa da hange iri guda amma yadda za su tunkare su zai bambanta.

Edo 2020: Babban dan takarar PDP ya janye wa Gwamna Obaseki
Edo 2020: Babban dan takarar PDP ya janye wa Gwamna Obaseki Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Ikhine ya kara da cewa ba wai zai ja baya bane, illa zai kasance a bayan mutumin da zai jagoranci jam’iyyar zuwa ga tafarkin nasara a ranar 19 ga watan Satumba.

Ya ce da shi da magoya bayansa sun yanke shawarar aiki tare da gwamnan domin tabbatar da inganci a jihar.

Da yake martani, Obaseki ya bayyana cewa da wannan lamari na siyasa a jihar, an kafa tarihi a kasar.

Ya bayyana cewa bayan shekaru 21 a wannan jumhuriya da ake ciki, damokradiyya ya samu sabon launi yayinda masu tunani suka shiga tsarin siyasa domin gyara lamarin siyasa da halin da kasar ke ciki.

KU KARANTA KUMA: Edo: APC za ta yi zaben fidda gwani, gwamnatin jihar ta sha alwashin hana taro

Gwamnan ya bayyana cewa ya dawo PDP ne saboda ya gane cewa PDP ce Edo kuma Edo ce PDP.

Ya yaba ma dan takarar da ya hada kai da jam’iyyar wajen gano baraka a PDP Edo da kuma tabbatar da ganin an magance matsalolin.

Obaseki ya bayyana cewa kamata ya yi ace gwamnati ta kasance don mutane ba wai don wasu yan tsiraru ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng