Kungiyar dattijan kudu ta shigar da karar Buhari a gaban kotu
Wasu kungiyoyi goma sha shidda na dattijan kudancin Najeriya sun shigar da karar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, bisa zarginsa da wofantar da yankin kudu a nadin manyan mukamai a gwamnatinsa.
Jagoran gamayyar kungiyoyin, dattijo Edwin Clark, ya shigar da karar a gaban wata kotun tarayya da ke Abuja.
A takardar karar, gamayyar kungiyoyin sun nemi a tilasta Buhari ya biya yankin kudu diyyar biliyan N50 saboda nuna musu banbanci, lamarin da suka ce ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya.
Sun bukaci kotu ta duba kundin tsarin mulki domin sanin abinda doka ta ce a sashe na 81(2) da sashe na 814(4) na kundin tsarin mulkin Najeriya domin fassara abinda suka kunsa dangane da nadin manyan mukamai a gwamnatin tarayya.
A cewarsu, shugaba Buhari ya sabawa kundin tsarin tsarin mulki wajen nadin manyan mukamai tun bayan hawansa mulki a shekarar 2015.
Kazalika, sun zargi shugaba Buhari da karbo rancen makudan kudade daga bankin Musulunci (IDB), bankin duniya, China, Japan da Jamus da sunan aiyukan raya kasa amma, sai, daga karshe ya karkatar dasu zuwa yankin arewa.
Sun bayyana hakan a matsayin cin amanar yankin kudancin Najeriya, a saboda haka sun nemi kotu ta bi musu hakkinsu.
DUBA WANNAN: Abinda yasa gwamnatin Buhari ta batawa Trump rai - Tsohon mai bashi shawara a kan tsaro
Manyan dattijan yankin kudu da suka rattaba kan hannu a kan takardar karar sun hada da shugaban kungiyar dattijan kabilar Yoruba; Reuben Fasoranti, takwaransa na kungiyar Ohaneze Ndigbo; John Nwodo, Pogu Bitrus, Ayo Adebanjo, Alowei Bozimo, Sarah Doketri, Chukwumeka Ezeife, Idongsit Nkanga, Kofoworola Bucknor-Akerele, Julie Umukoro, da Stephen Bangoji.
Sauran sun hada da Tijjani Babatunde, Rose Obuoforibo, Adakole Ijogi da Charles Nwakeaku.
Wadanda ake kara tare da Buhari sun hada da ministan shari'a; Abubakar Malami, magatakardar majalisa; Mohammed Sani-Omolori da hukumar kula da daidaito a rabon aiyuka da mukaman gwamnatin tarrayya.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng