Tsohon shugaban majalisa ya sanar da yin murabus daga zama mamba a jam'iyyar APC

Tsohon shugaban majalisa ya sanar da yin murabus daga zama mamba a jam'iyyar APC

Tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Edo, Alhaji Kabiru Adjoto, ya sanar da yin murabus daga zama mamba a jam'iyyar APC.

Da yake sanar da hakan ga wakilin kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a ranar Litinin, Adjoto ya ce ya yanke shawarar fita daga jam'iyyar APC bayan ya tuntubi 'yan uwa da abokansa na arziki da kuma dumbin magoya bayansa.

Ya ce ficewarsa daga jam'iyyar APC ya yi daidai da sashe da 95(i) na kundin tsarin mulkin APC.

A cewar Adjoto, ba a son ransa ya fice ya bar jam'iyyar APC ba, saboda ya shafe fiye da shekaru 10 a cikinta.

Sai dai, ya ce dole ya bar jam'iyyar APC saboda yana siyasa ne saboda mutanen jihar Edo, a saboda haka ba zai kasance a jam'iyyar da basa goyon baya ba. Ya kara da cewa murabus dinsa ya fara aiki na take.

Tsohon shugaban majalisa ya sanar da yin murabus daga zama mamba a jam'iyyar APC
Alhaji Kabiru Adjoto
Asali: Twitter

Legit.ng ta wallafa rahoton cewa Philiph Shaibu, mataimakin gwamnan jihar Edo, ya bi sahun maigidansa, gwamna Godwin Obaseki, wajen sanar da ficewarsa daga jam'iyyar APC.

Mista Shaibu ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar APC a ranar Talata, 16 ga watan Yuni, 2020.

DUBA WANNAN: An sanar da sakamakon zaben fidda dan takarar APC a jihar Edo

Obaseki, ya sanar da yanke shawarar ficewa daga jam'iyyar APC bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Gwamnan ya yi furucin hakan ne a kan hanyarsa ta fita daga fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya, Abuja.

Shugaban kwamitin tantance 'yan takara na jam'iyyar APC, Farfesa Jonathan Ayuba, shi ne ya bayar da sanarwar haramtawa Gwamna Obaseki tsayawa takara tun gabanin zaben fidda gwani.

Ayuba ya bayyana cewa an haramta wa Obaseki tsayawa takara ne sakamakon matsalar da aka gano akwai a tattare da takardunsa na makaranta.

A yau, Litinin, 22 ga watan Yuni, 2020, jam'iyyar APC, ta gudanar da zaben fidda dan takararta a zaben kujerar gwamnan jihar Edo, wanda za a yi a cikin watan Satumba.

Osagie Ize - Iyamu ya lashe zaben neman tikitin takarar kujerar gwamnan jihar Edo a karkashin inuwar jam'iyyar APC.

Ize - Iyamu ne ya yi wa jam'iyyar PDP takarar neman kujerar gwamnan jihar Edo a zaben da aka yi a shekarar 2016.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel