An sanar da sakamakon zaben fidda dan takarar APC a jihar Edo

An sanar da sakamakon zaben fidda dan takarar APC a jihar Edo

Osagie Ize - Iyamu ya lashe zaben neman tikitin takarar kujerar gwamnan jihar Edo a karkashin inuwar jam'iyyar APC.

A yau, Litinin, 22 ga watan Yuni, 2020, jam'iyyar APC, ta gudanar da zaben fidda dan takararta a zaben kujerar gwamnan jihar Edo, wanda za a yi a cikin watan Satumba.

Ize - Iyamu ne ya yi wa jam'iyyar PDP takarar neman kujerar gwamnan jihar Edo a zaben da aka yi a shekarar 2016.

An sanar da sakamakon zaben fidda dan takarar APC a jihar Edo
Osagie Ize - Iyamu
Asali: Facebook

Sai dai, ya sha kasa a hannun dan takarar jam'iyyar APC kuma gwamna mai ci a yanzu, Godwin Obaseki, wanda rikici tsakaninsa da shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya tilasta shi ficewa daga jam'iyyar.

DUBA WANNAN: Abinda yasa gwamnatin Buhari ta batawa Trump rai - Tsohon mai bashi shawara a kan tsaro

Hope Uzodinma, shugaban kwamitin zaben, ya sanar da cewa Ize-Iyamu ne ya zama zakara, kamar yadda sakamakon zaben da aka gudanar a fadin kananan hukumomin jihar Edo 18 ya nuna.

Ya samu jimillar kuri'u 27,838 yayin da na biyunsa, Dakta Odubu ya samu jimillar kuri'u 3,776, shi kuma wanda ya zo na uku, Mista Osaro Obaze, ya samu kuri'u 2,751.

Sakamakon zaben ya nuna cewa Ize-Iyamu zai fuskanci sauran 'yan takarar da zasu wakilci jam'iyyunsu a zaben kujerar gwamnan jihar Edo da za a yi ranar 19 ga watan Satumba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng