Sauya shekar mataimakin gwamnan Ondo ya tada kura a PDP

Sauya shekar mataimakin gwamnan Ondo ya tada kura a PDP

Sauya shekar mataimakin gwamnan jihar Ondo, Agboola Ajayi zuwa jam'iyyar PDP ya sa wasu daga cikin manema tikitin jam'iyyar don takara ke korafi a kan yadda ake bai wa masu sauya sheka fifiko a jam'iyyar.

A kalla 'yan takara takwas ne suka siya fam don nuna ra'ayin fitowa neman kujerar gwamnan jihar, ciki kuwa har da Eyitayo Jegede (SAN).

Majiya mai karfi ta ce 'yan takarar na zargin mataimakin gwamnan da nada shugaban kwamiti tare da mambobin kwamitin zaben fidda gwani a jihar.

Wata majiya ta ce Ajayi da kansa ya biya wani jirgi guda don dauko kwamitin gudanar da ayyuka na jam'iyyar PDP wanda ya samu jagorancin Prince Uche Secondus don karbarsa zuwa jam'iyyar a yau.

Har zuwa daren jiya Lahadi ba a tabbatar da zargin ba.

Sauya shekar mataimakin gwamnan Ondo ya tada kura a PDP
Sauya shekar mataimakin gwamnan Ondo ya tada kura a PDP Hoto: Dailypost
Asali: UGC

Daya daga cikin wadanda suka siya fam din kuma ya ki yin mubaya'a ya bayyana komawar Ajayi jam'iyyar PDP da ci gaba amma ccewa jam'iyyar za ta rikice matukar Ajayi ya samu yadda ake yadawa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawar sirri da gwamnonin APC

Dan takarar ya ce: "Ta yaya zai zo yanzun nan jam'iyyar sannan ya nemi nada shugaba da mambobin kwamitin zaben fidda gwani shi kadai? Ko saboda hakan ne ya yi hayar jirgi don ya kawo mambobin NWC don tarbarsa? Wannan cin mutunci ne.

"Mu zuba ido mu ga abinda zai faru amma su sani, mu ba sakarkaru bane a wannan jam'iyyar,"

Amma a takardar da kakakin Ajayi, Babatope Okeowo ya fitar, ya musanta cewa shi NWC ta fitar a matsayin dan takararta. Ya ce tsegumi da rade-radi basu damunsa.

Ajayi baya ta masu neman bata masa suna ta hanyar haddasa gaba tsakaninsa da 'yan PDP.

A baya Legit.ng ta kawo cewa mataimakin gwamnan jihar Ondo, Hon. Agboola Ajayi, ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Agboola ya sanar da barinsa jam'iyyar mai mulki a ranar Lahadi, 21 ga watan Yuni, jaridar Leadership ta ruwaito.

Agboola wanda ya sanya hannu a takardar barinsa jam’iyya mai mulki a Ward 2, Apoi Na karamar hukumar Ese-Odo da ke jihar, ya gaggauta daukar takardar zama dan jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP).

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng