Jihar Borno ta bukaci Gwamnati ta rabawa Matasanta 300 aiki - Kwamishina

Jihar Borno ta bukaci Gwamnati ta rabawa Matasanta 300 aiki - Kwamishina

Gwamnatin jihar Borno ta bada shawarar a dauki matasa 300 domin a ba su abin-yi a karkashin ma’aikatun gwamnati da na ‘yan kasuwa da ke cikin jihar da kuma wajen jihar.

Kwamishinan kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire a Borno, Babagana Mustafa ya bayyana wannan a ranar Lahadi, 21 ga watan Yuni, 2020, lokacin da ya zanta da 'yan jarida.

Injiniya Babagana Mustafa ya yi hira da ‘yan jarida ne domin ya bayyan irin nasarorin da ma’aikatarsa ta samu a cikin watanni goma da ta yi daga lokacin da aka kafa ta.

A cewar Babagana Mustafa, ya ce wadannan matasa su na cikin wadanda su ka yi rajista a shafin da ma’aikatar ta bude domin samun alkaluman wadanda ba su da sana’a a Borno.

Mustafa ya ce gwamnati ta dauki sunayen wadanda su ke neman abin yi ne domin a samu damar cike guraben damammakin da jihar Borno ta ke da su a ma’aikatun da ke kasar.

Haka zalika wannan alkaluma za su taimaka wajen daukar matasan da za a koyawa sana’a a jihar. Kwamishinan ya nuna wannan kadan kenan daga cikin gwamnatin APC.

KU KARANTA: An kama 'Dan Najeriya da laifin damfarar mutane a Amurka

Jihar Borno ta bukaci Gwamnati ta rabawa Matasanta 300 aiki - Kwamishina
Gwamnan Jihar Borno Babagana Zulum
Asali: Twitter

Mai girma Kwamishinan ya shaidawa manema labarai cewa wasu daga cikin wadannan mutane da aka zaba sun samu aiki, yayin da wasu su ke samun horon sana’ar aikin hannu.

“Wannan alkaluma za su bada damar yin horo da koyar da aiki domin a inganta kwarewar aikin matasan jihar Borno.” Inji Kwamishinan na kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire.

Injiniya Mustafa ya ce gwamna Farfesa Babagana Zulum ne ya kafa wannan ma’aikata a 2019 domin ya taimaka wajen bunkasa cigaban tattalin arziki da cigaban jihar Borno.

Kwamishinan ya ce an kafa cibiyar koyar da sana’o’i a garin Maiduguri, kuma za a gyara duk ire-iren wadannan cibiyoyi da makarantun koyar da ayyukan hannu da ke fadin jihar.

“Cibiyoyin na VEI za su bada hurumin horas da wadanda aka sallama daga makaranta ko masu neman koyon sana’ar hannu domin su rike kansu, ko matasan da ke neman aiki.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel