APC ta fara gudanar da zaben fidda gwanin takara na gwamnan jihar Edo

APC ta fara gudanar da zaben fidda gwanin takara na gwamnan jihar Edo

Rahotanni da ke zuwa mana a yanzu sun nuna cewa, an fara zaben fidda gwanin takarar gwamnan jihar Edo na jam'iyyar APC kamar yadda aka kayyade tun a baya.

Yanzu dai ta tabbata cewa ana gudanar da zaben ne kai tsaye ta hanyar 'yar tinke ko kuma kato ya biyo bayan kato a maimakon gudanar da zaben ta hanyar amfani da wakilai.

Za a gudanar da zaben ne a mazabu 192 cikin kananan hukumomi 18 da ke fadin jihar.

A ranar Alhamis ta makon jiya ne wata kotun daukaka kara da ke zamanta a Benin, ta yanke hukuncin gudanar da zaben kai tsaye ta hanyar 'yar tinke.

Jaridar The Nation ta wallafa cewa, an fara gudanar da zaben ne a mazaba ta biyar da ke harabar makarantar Firamaren St. Saviours a karamar hukumar Ikpoba/Okha da ke birnin Benin.

Masu kada kuri'a sun kiyaye dokar bayar da tazara da yin nesa-nesa da juna tare da sanya takunkumin rufe fuska kamar yadda gwamnan jihar Godwin Obaseki ya ba da umarni.

APC ta fara zaben fidda gwanin takara na gwamnan jihar Edo
Hakkin Mallakar Hoto: Jaridar The Nation
APC ta fara zaben fidda gwanin takara na gwamnan jihar Edo Hakkin Mallakar Hoto: Jaridar The Nation
Asali: Twitter

KARANTA KUMA: Ministan Shari'a ya ba da sunayen mutum 3 da za su maye kujerar Magu

APC ta fara zaben fidda gwanin takara na gwamnan jihar Edo
Hakkin Mallakar Hoto: Jaridar The Nation
APC ta fara zaben fidda gwanin takara na gwamnan jihar Edo Hakkin Mallakar Hoto: Jaridar The Nation
Asali: Twitter

Jami'an Tsaro da aka tanada yayin zaben fidda gwanin takara na gwamnan jihar Edo
Hakkin Mallakar Hoto: Jaridar The Nation
Jami'an Tsaro da aka tanada yayin zaben fidda gwanin takara na gwamnan jihar Edo Hakkin Mallakar Hoto: Jaridar The Nation
Asali: Twitter

Baya ga jami'an Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC da aka tanada, an kuma jibge jami'an tsaro musamman na 'yan sanda da DSS domin jiran ko ta kwana da ba a fatan ta auku.

Manema takara biyu ne kacal jam'iyyar APC ta amince da su a zaben na 'yar tinke da ya fara gudana. Sun hadar da Fasto Osagie Ize-Iyamu da kuma Dr. Pius Odubu.

Ize Iyamu shi ne wanda ya fito takarar gwamnan jihar Edo karkashin jam'iyyar PDP a shekarar 2016, inda a watan Dasumba ya sauya sheka zuwa APC.

Jam'iyyar APC ta sahalewa Ize-Iyamu yin takarar gwamnan jihar Edo a ranar 21 ga watan Mayu.

Shi kuwa Odubu, ya kasance mataimakin gwamnan jihar a lokacin da Kwamared Adams Oshiomhole ke rike da akalar jagoranci a jihar.

Daga cikin 'yan kwamitin sa ido kan zaben da aka zaba sun hadar da Farfesa Mustapha Bello, Dr. Kayode Ajulo, Umar Ahmed, Nasiru Junju da Rasaq Bamu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel