Edo: APC za ta yi zaben fidda gwani, gwamnatin jihar ta sha alwashin hana taro
Jam'iyyar APC a jihar Edo ta ce za ta yi tsarin kato bayan kato wajen zaben fidda gwani duk da gwamnatin jihar ta hana taron jama'a masu yawa.
Jam'iyyar ta ce bata bukatar gwamnatin jihar ta amince mata don yin zaben fidda gwanin da take so.
Idan za mu tuna, a ranar 28 ga watan Mayun 2020 ne Gwamna Obaseki ya saka hannu a kan takardar da tace bai amince da wani nau'in zaben fidda gwani da zai tara jama'a a wuri daya ba. Kuma a babban birnin jihar na Benin ya amince a yi.
Wani jigo a sashen jam'iyyar na Oshiomhole, Henry Idahagbon, ya ce jam'iyyar ta shirya zaben fidda gwaninta.
" Nan da ranar Litinin, za mu yi zaben fidda gwani na tsarin kato bayan kato kuma za mu fitar da dan takararmu. A halin yanzu muna da dan takara, za mu tabbatar da shi ne.
"Ko wacce irin takarda gwamnan ya sa hannu, shi ya fara take ta don mun ganshi da sama da mutum 500 a cikin satin nan. Don haka idan ya take doka, dole mu bi sahunsa."
Bangaren jam'iyyar wanda ke karkashin Aslem Ojezua ya ce suna sane da cewa APC za ta yi zaben fidda gwaninta a jihar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Ojezua na daya daga cikin magoya bayan Obaseki duk da komawar gwamnan PDP. Ojezua na nan a jam'iyyar APC.
KU KARANTA KUMA: Hankalinmu ba zai kwanta ba saboda talaka bashi da walwala - Sanata Ndume
"Wasa suke yi. Wanda ya shirya kwamitin zaben fidda gwanin ba shi bane mukaddashin shugaban jam'iyyar. Saboda haka ne muka yi watsi da kwamitin a yayin da aka kafa shi. Victor Giadom ne zai sanar da mu abinda za mu yi.
"Zan iya cewa suna bata wa kansu lokaci ne. Duk abinda za su yi da ya danganci zaben fidda gwani na banza ne."
Amma kuma, gwamnatin jihar Edo ta ce dole za ta saka doka don hana yaduwar annobar korona a jihar. Ta yi kira ga jam'iyyun siyasa da su kiyaye dokokin dakile yaduwar annobar a jihar matukar za su yi zaben fidda gwani.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng