COVID-19: Gudumuwa sun sa SERAP ta na karar Ma’aikatar lafiya da NCDC

COVID-19: Gudumuwa sun sa SERAP ta na karar Ma’aikatar lafiya da NCDC

Kungiyar SERAP ta kai karar Ministan lafiya, Dr. Osagie Ehanire da shugaban hukumar NCDC na kasa, Dr. Chikwe Ihekweazu kotu a kan gudumuwar kudin da aka samu wajen yaki da COVID-19.

Wannan kungiya mai zaman kanta, ta shigar da kara a kotu ne saboda gazawar ma’aikatar lafiyar da hukumar NCDC mai takaita yaduwar cututtuka ta gaza bayani game da kudin tallafin da kasar ta samu.

Jaridar Desert Herald ta ce an gabatar da wannan kara ne a makon da ya gabata a wani babban kotun tarayya da ke garin Abuja. Kungiyar ta nemi a tursasawa ma’aikatar lafiya ta fadi duk tallafin da aka bada.

SERAP ta na so ma’aikatar lafiya da NCDC su wallafa bayani a game da yadda aka kashe kudin da gwamnatin tarayya da jihohi da kuma masu zaman kansu su ka bada wajen ganin an yaki annobar.

Bayan haka, SERAP ta nemi kotu ta ba gwamnati umarnin bayyana adadin manyan mutanen da aka yi wa gwajin kwayar cutar a kasar, da kuma sunayen wadannan mutane da ke killace a dalilin haka.

KU KARANTA: Likitoci sun janye yajin aiki bayan 'yan kwanaki

COVID-19: Gudumuwa sun sa SERAP ta na karar Ma’aikatar lafiya da NCDC
Ministan lafiya Dr. Osagie Ehanire
Asali: Facebook

A shari’a mai lamba ta FHC/ABJ/CS/616/2020, SERAP ta na zargin gwamnati da kin yi wa jama’a bayanin kudin da aka kashe wajen yaki da wannan annoba a Najeriya.

Rahoton ya bayyana cewa kungiyar ta nemi a fito da sunayen ya-ku-bayin da aka yi wa gwajin. SERAP ta na son sanin sunayen wadanda aka yi wa gwaji bayan ‘yan siyasa da sauran mala’u.

A cewar kungiyar, yin gaskiya a game da yadda ake kashe gudumuwar da aka bada zai rage satar kudin talakawa da kuma damar wawurar dukiyar al’umma, sannan hakan zai rage yaduwar cutar a kasar nan.

Za a karfafa hukumomi idan mutanen Najeriya su ka samu masaniya a game da yadda ake batar da gudumuwar yaki da annobar COVID-19.

A watan Maris, SERAP ta koka da cewa rashin yin gaskiya wajen sha’anin kashe gudumuwar da aka ba gwamnati zai taimakawa ma’aikatar lafiya wajen karkatar da kudi da dukiyar talakawa, da kuma jawo rashin rayuka.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel