Shugaban kasa ya yi na’am da binciken zargin da ake kan Magu a Hukumar EFCC

Shugaban kasa ya yi na’am da binciken zargin da ake kan Magu a Hukumar EFCC

Jaridar Desert Herald ta ce kafar mukaddashin shugaban EFCC, Ibrahim Magu, ta fara ficewa daga hukumar bayan fadar shugaban kasa ta bada umarnin a soma gabatar da bincike a kansa.

Hakan na zuwa ne bayan Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin Najeriya, Abubakar Malami SAN, ya jefi shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon-kasa da aikata laifuffuka a ofis.

Majiya daga fadar shugaban kasar ta bayyanawa jarida cewa Muhammadu Buhari ya yi na’am da maganar fara binciken shugaban hukumar da ke binciken, har kuma ta kai ana maganar Ibrahim Magu ya ajiye aiki.

Desert Herald ta ke cewa akwai yiwuwar Mista Ibrahim Magu ya sauka daga kan kujerarsa domin a yi bincike a hukumar EFCC, wannan zai bada damar Mohammed Umar Abba ya dare kan kujerarsa.

Mohammed Umar Abba shi ne babban darekta a hukumar wanda zai rike kujerar rikon kwarya bayan Magu. A karshe ana tunanin Kwamishinan ‘yan sanda, Bala Ciroma ne zai zama sabon shugaban EFCC.

CP Bala Ciroma Kwamishinan ‘yan sanda ne a babban birnin tarayya Abuja, kuma ya na cikin wadanda Abubakar Malami ya kai sunansa gaban shugaban kasa, a wani kaulin ana fifita nadinsa.

KU KARANTA: Buhari ya aikawa Majalisa sunaye 200, ya ki waiwayar Shugaban EFCC

Shugaban kasa ya yi na’am da binciken zargin da ke kan Magu a Hukumar EFCC
Shugaban kasa da Ministan shari'a Hoto: Aso Villa
Asali: UGC

Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci a nada kwamiti da zai binciki Ibrahim Magu ne saboda nauyin zargin da Ministan shari’a ya jefesa da su, sai dai shugaban kasar ya na gudun daukar matakin gaggawa.

Muhammadu Buhari zai tabbatar ya nada kwamiti mai karfi da zai binciki zargin badakalar da ke kan hukumar domin a bi diddikin lamarin. Fadar shugaban kasa ba ta tabbatar da hakan ba tukuna.

Wanda ya samu masaniya ya ce tsohon alkalin babban kotun daukaka kara, Ayo Salami ne zai jagoranci kwamitin binciken. Sauran ‘yan kwamitin sun hada da mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaro.

Shugabannin hukumar DSS, NIA da Sufetan ‘Yan Sanda da kuma Ministan shari’a su na cikin wadanda za su yi wannan bincike, za kuma su aikawa shugaban kasa rahoto nan da makonni biyu.

Da aka tambayi Mallam Garba Shehu game da lamarin, ya nuna cewa bai da labari Haka zalika jaridar ba ta yi nasarar tuntubar mai magana da yawun bakin EFCC, Dele Oyewale ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel