Yanzu Yanzu: Mataimakin gwamnan jihar Ondo ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

Yanzu Yanzu: Mataimakin gwamnan jihar Ondo ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

- Yayinda zaben gwamnan Ondo ke gabatowa, yan takarar sun yanke shawarar jan layi domin fafatawa da junansu

- Mataimakin gwamnan jihar Ondo, Agboola Ajayi ya sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki yan watanni bayan raba jiha da ubangidansa

- Tuni Agboola ya koma jam’iyyar Peoples Democratic Party yayinda yake shirin kwace jihar daga hannun Gwamna Rotimi Akeredolu

Mataimakin gwamnan jihar Ondo, Hon. Agboola Ajayi, ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Agboola ya sanar da barinsa jam'iyyar mai mulki a ranar Lahadi, 21 ga watan Yuni, jaridar Leadership ta ruwaito.

Agboola wanda ya sanya hannu a takardar barinsa jam’iyya mai mulki a Ward 2, Apoi Na karamar hukumar Ese-Odo da ke jihar, ya gaggauta daukar takardar zama dan jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP).

Yanzu Yanzu: Mataimakin gwamnan jihar Ondo ya sauya sheka daga APC zuwa PDP
Yanzu Yanzu: Mataimakin gwamnan jihar Ondo ya sauya sheka daga APC zuwa PDP Hoto: Dailypost
Asali: UGC

Dangantakar da ke tsakanin Ajayi da gwamnan jihar, Oluwarotimi Akeredolu ya yi tsami yan watanni da suka gabata.

Legit.ng ta tuna cewa Agboola da ubangidan nasa sun raba jiha ne kan yadda za a tafiyar da jihar sannan lamarin ya yi kamari ne a lokacinda Gwamna Akeredolu ya kaddamar da kudirinsa na sake tsayawa takara a karo na biyu.

KU KARANTA KUMA: A karon farko: Gwamnan Bauchi ya yi martani a kan zargin damfara da ICPC ke masa

A ranar Asabar, 20 ga watan Yuni, sabanin dake tsakanin gwamnan da mataimakinsa ya sake daukar zafi, yayinda aka yi zargin ccewa Gwamna Akeredolu ya hana Agboola fita daga jihar Ondo da motocin gwamnati.

A wani labarin kuma, mun ji a baya cewa rikicin cikin gida na jam'iyyar APC ya raba kan gwamnoni zuwa gida biyu. Yayin da gwamnoni 13 ke goyon bayan kwamitin gudanar da ayyuka karkashin jagorancin Abiola Ajimobi, wasu gwamnoni bakwai na sukar hakan.

Bakwai daga cikin gwamonin wadanda suka kira kansu da "masu gyara" sun kosa don kwace tafiyar da jam'iyyar kafin zuwan zaben 2023.

Gwamnonin 13 sun kira bakwai din da "masu mafarki da rana tsaka".

Wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a jam'iyyar a halin yanzu suna bukata tare da rokon zaman lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel