A karon farko: Gwamnan Bauchi ya yi martani a kan zargin damfara da ICPC ke masa

A karon farko: Gwamnan Bauchi ya yi martani a kan zargin damfara da ICPC ke masa

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi, ya ce bai karya wata doka ba a kan kadarar miliyoyin naira da hukumar yaki da rashawa ta ICPC gano yana da ita.

A wata takarda da hukumar ta fitar a yanar gizo a ranar Talata, ta sanar da kace kadarar wacce ake amfani da ita a matsayin Zinaria International School a Abuja.

ICPC ta ce bincike ya nuna cewa gwamnan ya bai wa kansa kadarar ne a lokacin da yake ministan babban birnin tarayya Abuja duk da cewa mallakin ma'aikatar noma da kiwo ce.

Amma kuma Mukhtar Gidado, mai magana da yawun gwamnan jihar Bauchi ya ce ICPC na bibiyar gwamnan da iyalansa.

Ya ce tun kafin gwamnan ya yi ministan tarayya makarantar ke nan. Tun a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

A karon farko: Gwamnan Bauchi ya yi martani a kan zargin damfara da ICPC ke masa
A karon farko: Gwamnan Bauchi ya yi martani a kan zargin damfara da ICPC ke masa Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Gidado ya ce gwamnan bai take wata doka ba balle tozarta rantsuwar da yayi. Ya ce makarantar ta kara girma ne bayan da masu ita tare da masu hannayen jari a cikinta suka nemi fili ta hanyar da ya dace.

"Mun musanta labarin ICPC gaba dayansa a kan gwamna Bala Mohammed. Bai take wata doka ba a kundun tsaron mulki ko kuma rantsuwarsa," takardar tace.

"Zinaria International School an kafa ta ne tun kafin Sanata Bala Mohammed ya zama ministan tarayya.

"Kamar yadda kowanne kasuwancin hadin guiwa ke yi. Sun samu karin fili ta hanyar da ya dace. Masu filin 'yan Najeriya na kuma suna da damar bin hanyar da ta dace don samun shi."

A gefe guda, jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Bauchi, ta ce rahotannin kwace kadarar gwamnan Bala Mohammed ta miliyoyin naira da ICPC tayi ya isa ya zama hujjar da za ta sa ya yi murabus a matsayin gwamnan jihar ko a tsigesa.

KU KARANTA KUMA: Rikicin APC: Gwamnoni 13 sun goyi bayan NWC, 7 na sukarsu

Jam'iyyar APC ta yi kira ga gwamnan da ya sauka daga mulkin jihar a mutunce.

Wannan bukatar na kunshe ne a wata takarda da jaridar The Nation ta samu bayan shugaban kwamitin yada labarai na jam'iyyar APC a jihar, Kwamared Sabo Mohammed da sakatare Mallam Sa'adu Umar suka sa hannu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel