Wasu gwamnonin APC na goyon bayana - Obaseki

Wasu gwamnonin APC na goyon bayana - Obaseki

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya ce har yanzu wasu gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na goyon bayansa duk da cewar ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Obaseki ya sanar da sauya shekarsa zuwa PDP a ranar Alhamis biyo bayan hana shi takara a zaben fidda gwanin APC.

Kwamitin APC ya bayyana aibin takardunsa a matsayin dalilin hana shi takarar kujerar.

Amma da yake magana da manema labarai bayan tantance shi da sabuwar jam’iyyarsa ta yi, gwamnan ya ce wadannan takardu da APC ta yi watsi dasu shine ya gabatar wa da PDP domin tantance shi ba tare da ya fuskanci kalubale daga kwamitin ba.

Wasu gwamnonin APC na goyon bayana - Obaseki
Wasu gwamnonin APC na goyon bayana - Obaseki Hoto: Vanguard
Asali: UGC

“Akwai adalci a tantancewar, an yi shi cike da kwarewa. Kuna iya gani kuma na gabatar da dukkanin takarduna- na makarantar sakandare, babban makaranta, jami’a da kuma takardar kammala bautar kasana, domin su duba su gani idan akwai aibu a tattare da su.

"Kuna iya tambayar kwamitin tantancewa idan akwai wani aibu a kowanne daga cikinsu.”

A bangaren goyon baya da yake samu, ya ce: “Ina godiya ga Allah cewa ina samun goyon bayan kasa ba wai na takwarorina daga APC ba kadai. Ina ganin goyon bayan daga kasa ne baki daya. Akwai dattawa wadanda basa siyasa, akwai sarakunan gargajiya.

“Ina da mutane daga bangarori daban-daban wadanda suka zo don goyon bayana. Gaba daya, ina ganin yan Najeriya gaba daya sun kasance mutane masu adalci. Mutane ne da basa yarda da rashin adalci.

KU KARANTA KUMA: Karin mutum 661 sun kamu da korona a Najeriya

“Daga abunda na gani a yan makonni da watannin da suka gabata, goyon bayan yana da yawa. Ba wai daga gwanonin APC bane kawai.”

Idan har ya samu tikitin PDP, hakan na nufin za su sauya inuwa tare da abokin adawarsa a 2016. Osagie Ize-Iyamu, wanda ya kayar a zaben gwamna da ya gabata, ya koma APC kuma yana da goyon bayan shugabannin jam’iyyar.

Adams Oshimhole, Shugaban jam’iyyar APC da aka dakatar yana goyon bayan Ize-Iyamu ne.

Oshiomhole ne ya kawo Obaseki kan karagar mulki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel