Tsaro: Gwamnonin arewa sun yi taro, sun fitar da sabbin tsare-tsare

Tsaro: Gwamnonin arewa sun yi taro, sun fitar da sabbin tsare-tsare

Mambobin kungiyar gwamnonin arewa sun yi taro a ranar Alhamis, 18 ga watan Yuni don duba yanayin rashin tsaro da ya addabi yankin.

Taron da aka yi ta yanar gizo wanda shugaban kungiyar gwamnonin, Simon Lalong ya jagoranta, ya jajanta a kan karuwar rashin tsaro a yankin arewa.

A yayin taron, gwamnonin sun fara zantawa a kan matakan da za'a dauka a kan rashin tsaron.

Daga cikin matakan, sun amince da kafa kwamitin kula da tsaro a arewa wanda zai dinga duba al'amuran tabbatar da tsaro a yankin.

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, shi aka nada shugaban kwamitin yayin da Gwamna Matawalle na jihar Zamfara da takwaransa na Gombe, Muhammad Yahaya suka zama mambobi.

Daya kwamitin ya samu shugabancin gwamnan jihar Filato, Simon Lalong da gwamna Ahmadu Fintiri, Abubakar Bello da Aminu Tambuwal.

Tsaro: Gwamnonin arewa sun yi taro, sun fitar da sabbin tsare-tsare
Tsaro: Gwamnonin arewa sun yi taro, sun fitar da sabbin tsare-tsare Hoto: Thisdaylive
Asali: UGC

Sune za su tuntubi malaman addinai, sarakunan gargajiya da shugabannin yankuna a arewa.

Kamar yadda mai magana da yawun Gwamna Lalong ya sanar, kwamitin zai tabbatar da an saka bangarori da yawa wurin shawo kan matsalar tsaro a arewa.

Gwamnonin sun yanke hukuncin saka 'yan banga, mafarauta da kuma kungiyoyin yankuna don tsara tsaron yankin tare da inganta rahotannin sirri.

A saboda haka suka yi kira ga gwamnatin tarayya da ta duba tsaron ECOWAS na barin shige da fice ta iyakokin kasar nan musamman a arewa.

A yayin jinjinawa gwamnatin tarayya a kan kokarin shawo kan matsalar tsaro, sun yi kira ga gwamnatin da ta inganta tare da tallafawa don kawo karshen ayyukan 'yan bindiga.

Sun amince da duba tsarin tattaunawa tare da amfani da tsarin dakarun soji wajen shawo kan kalubalen tsaro a arewa.

KU KARANTA KUMA: COVID-19: Akwai yuwuwar mu sake garkame Kaduna - El-Rufai

A kan hare-haren kwanan nan, gwamnonin sun jajantawa wadanda abun ya shafa, sun yi kira ga kungiyoyi da su kwantar da hankalinsu.

Sun tabbatar wa da mazauna yankin cewa kungiyar, gwamnatocin jihohi da na tarayya na kokarin shawo kan matsalar.

A gefe guda Legit.ng ta rahoto cewa, a ranar Alhamis jami'an tsaro sun damke matasa masu tarin yawa sakamakon zanga-zangar lumana da suka yi saboda rashin tsaron da ya addabi jihar Katsina.

Daliban da aka kama da yawansu 'yan makarantun gaba da sakandare ne wadanda suka fito tituna suna bukatar murabus din manyan jami'an gwamnatin.

Daliban sun kammala zanga-zangar ne a tsakiyar garin Katsina inda suka yi tattaki har ofishin 'yan sanda.

Yayin tabbatar da kamen, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah ya ce "tabbas mun kama da yawa daga cikinsu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel