COVID-19: Akwai yuwuwar mu sake garkame Kaduna - El-Rufai

COVID-19: Akwai yuwuwar mu sake garkame Kaduna - El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai a ranar Laraba ya ja kunnen cewa akwai yuwuwar ya sake saka dokar hana walwala ga jama'ar jihar matukar aka ci gaba da yin watsi da dokokin dakile yaduwar cutar coronavirus.

Ya yi karin bayani da cewa, "idan yawan masu kamuwa da cutar ya sha karfin cibiyoyin lafiyarmu da ma'aikatanmu, za mu sake rufe jihar."

Gwamnan ya sanar da hakan ne yayin kaddamar da abun hawa na gwaji da USAID ta bai wa jihar.

Ya ce ya dage dokar hana walwalar ne saboda yana da tabbacin jihar na da kayan gwaji da dakunan gwaji isassu, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

COVID-19: Akwai yuwuwar mu sake garkame Kaduna - El-Rufai
COVID-19: Akwai yuwuwar mu sake garkame Kaduna - El-Rufai Hoto: The Cable
Asali: UGC

"Ina kira ga jama'ar jihar Kaduna da su kiyaye dokokin da aka saka tare da rage yawan yawon da suke yi saboda idan ya zama dole a sake rufe jihar, ba za mu yi kasa a guiwa ba," yace.

Yayin jawabi game da abun gwajin, El-Rufai ya ce an samar da manyan na'urori. Ya ce dakin gwajin tafi-da-gidanka za a iya amfani da shi wurin gwajin wasu cutuka masu tarin yawa. Da farko an kawo shi kasar nan ne don gwajin tarin t.b.

"Amma sakamakon barkewar annobar Coronavirus, an bamu damar gwajinta. Ta dade a jihar kuma an gwada samfur a kalla 200 da ita wanda mafi akasarinsu suna dauke da ita.

KU KARANTA KUMA: Kurunkus: 'Yan takara biyu na APC sun janye, Ize-Iyamu kadai zai yi zaben fidda gwani

"An yi amfani da na'urar ne sosai wajen gwajin jama'a kuma sakamakon ya dan tsoratar domin an samu kaso 16 da suka harbu a garuruwan a yayin da aka yi gwajin.

"Wadannan sun kasance garuruwa da ke iyaka da jihohi masu makwabtaka, wadanda annobar ta barke sosai a cikinsu," ya kara da cewa.

A baya mun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce bayan sassauta dokar kulle da yayi a jihar Kaduna, mataki na gaba shine kiyaye yaduwar annobar korona wacce take hannun mutane.

El-Rufai ya roki jama'ar jihar da su dauka dawainiyar yaki da yaduwar cutar korona. Ya ce kada a mayar da kokarin da yayi a baya ta hanyar kin kiyaye dokokin hana yaduwar cutar.

Gwamnan wanda ya mika wannan rokon a ranar Talata, ya mika sakon godiyarsa ga jama'ar jihar Kaduna a kan yadda suka yi hakurin watanni biyu da rabi wurin dakile annobar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel