Kurunkus: 'Yan takara biyu na APC sun janye, Ize-Iyamu kadai zai yi zaben fidda gwani

Kurunkus: 'Yan takara biyu na APC sun janye, Ize-Iyamu kadai zai yi zaben fidda gwani

Osagie Ize-Iyamu, zai zama dan takarar gwamna guda a karkashin jam'iyyar APC a zaben ranar 19 ga watan Satumban 2019.

Ize-Iyamu wanda ya sha mugun kaye a hannun Godwin Obaseki, gwamnan jihar Edo a shekaru hudu da suka gabata, yana samun goyon bayan Adams Oshiomhole, dakataccen shugaban jam'iyyar APC na kasa.

Jaridar The Cable ta gano cewa, Osaro Obazee, wanda yayi takarar kujerar dan majalisa jihar a 2019 da Pius Odubu, tsohon mataimakin Gwamnan jihar, sun yi mubaya'a tare da nuna goyon bayansu ga Ize-Iyamu.

Kafin su bada goyon bayansu ga Ize-Iyamu, sune ragowar 'yan takara biyu da za su kara da shi a zaben fidda gwani.

Kurunkus: 'Yan takara biyu na APC sun janye, Ize-Iyamu kadai zai yi zaben fidda gwani
Kurunkus: 'Yan takara biyu na APC sun janye, Ize-Iyamu kadai zai yi zaben fidda gwani Hoto: The Guardian
Asali: UGC

'Yan takara shida ne suka nuna bukatar tsayawa takara a zaben fidda gwanin da za a yi a ranar 22 ga watan Yuni amma uku tak suka tsallake matakin tantancewa.

KU KARANTA KUMA: Sabon shugaban jam'iyyar APC na rikon kwarya, Abiola Ajimobi, ya rasu

Obaseki, Chris Ogiemwonyi, tsohon minista da Mathew Iduoriyekemwen duk an hana su fitowa takarar.

Bayan hana Obaseki fitowa takarar, ya bar jam'iyyar APC sannan ya yi ganawar sirri da Uche Secondus, shugaban jam'iyyar adawa ta PDP.

Ana tsammanin zai koma jam'iyyar PDP koyaushe daga yanzu.

Idan hakan ta faru, za ta zamana Obaseki sun yi musayar jam'iyya da abokin hamayyarsa a zaben gwamnonin jihar da ya gabata.

A ranar Alhamis, APC ta rantsar da kwamitin zaben jihar Edo da na daukaka kara wanda yanzu ya zamana tamkar shan ruwa ga Ize-Iyamu.

KU KARANTA KUMA: Rikicin APC babban kalubale ne ga ginin da ka fara - Lukman ga Buhari

Abiola Ajimobi, mukaddashin shugaban jam'iyyar APC, wanda ya samu wakilcin Hillard Eta, mataimakin shugaban jam'iyyar na kudu maso kudu, ya bai wa kwamitin umarnin tabbatar da nasarar duk wanda ya samu tikitin takarar gwamnan karkashin jam'iyyar APC.

Kwamitin mutum bakwai na zaben fidda gwanin ya samu shugabancin Hope Uzodinma, gwamnan jihar Imo da Ajibola Bashiru, a matsayin sakataren kwamitin.

Kwamitin daukaka karar zaben ya samu shugabancin Dr. Yusuf Nawai da Dr. Kayode Ajulo a matsayin sakatare.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel