Yanzu-yanzu: PDP ta daga ranar yin zaben fidda gwani a Edo
- Jam'iyyar PDP ta dage zaben fidda gwaninta na gwamnan jihar Edo
- Da farko an sanya ranar 22 ga watan Yuni a matsayin ranar zaben fidda gwanin amma aka dage zuwa 23 ga watan Yuni
- An tattaro cewa hakan baya rasa nasaba da yunkurin da Gwamna Godwin Obaseki na jihar ke yi na komawa cikinta bayan ya bar APC
Jam'iyyar Peoples Demoratic Party (PDP) ta dage zaben fidda gwani na gwamnan jihar Edo da za ta yi.
Mai magana yi da yawun jam'iyyar, Koma Ologbodiyan ya sanar da hakan a wata wallafa da yayi a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis.
An saka ranar Litinin 22 ga watan Yuni a matsayin ranar zaben fidda gwanin. Amma an dage zuwa ranar Talata, 23 ga watan Yuni.
Duk da babu wani bayani game da dalilin dage zaben fidda gwanin, an gano cewa akwai yuwuwar shirin komawar Gwamna Godwin Obaseki zuwa jam'iyyar ne a kowanne lokaci daga yanzu.
KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Ajimobi ya rantsar da kwamitin zaben fidda gwani na APC a Edo
Idan za ku tuna a baya Legit.ng ta kawo maku cewa shugabannin jam'iyyar PDP za su yi taro a ranar Alhamis don tattaunawa a kan makomar gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, wanda ke neman tikitin zarcewa a kujerarsa.
Majiya mai karfi ta ce babbar jam'iyyar adawar ta ce za ta yi taron ne don sauraron rahotanni daga dukkan shugabannin jam'iyyar da gwamnan ya samu ganawa da su a kwanaki biyar da suka gabata.
Obaseki ya gana da Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da Gwamna Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom a ranakun karshen mako kafin ya sanar da fitarsa daga jam'iyyar APC wacce ta hana shi fitowa zaben fidda gwani.
Hakazalika, mataimakinsa, Philip Shaibu ya fice daga jam'iyyar APC tare da sauke tutocinta da ke gidan gwamnati a Benin.
Obaseki ya samu tattaunawa da shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Uche Secondus da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal.
Yadda jam'iyyar za ta bashi tikitinta na takarar gwamnan jihar Edo ne babban abun tattaunawa a yau, majiya ta tabbatar kuma jaridar The Nation ta ruwaito.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng