Rashin tsaro: 'Yan sanda sun kama daliban da suka yi zanga-zanga a Katsina

Rashin tsaro: 'Yan sanda sun kama daliban da suka yi zanga-zanga a Katsina

A ranar Alhamis jami'an tsaro sun damke matasa masu tarin yawa sakamakon zanga-zangar lumana da suka yi saboda rashin tsaron da ya addabi jihar Katsina.

Daliban da aka kama da yawansu 'yan makarantun gaba da sakandare ne wadanda suka fito tituna suna bukatar murabus din manyan jami'an gwamnatin.

Daliban sun kammala zanga-zangar ne a tsakiyar garin Katsina inda suka yi tattaki har ofishin 'yan sanda.

Rashin tsaro: 'Yan sanda sun kama daliban da suka yi zanga-zanga a Katsina
Rashin tsaro: 'Yan sanda sun kama daliban da suka yi zanga-zanga a Katsina Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Yayin tabbatar da kamen, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah ya ce "tabbas mun kama da yawa daga cikinsu.

"Sun fito tituna suna bukatar sakataren gwamnatin jihar yayi murabus. Don haka bamu san wanda ya tsara musu hakan ba.

"A shari'ance babu gaskiya a zagi ja'ami'an gwamnatin. Hakan babban laifi ne kuma ba za mu kyalesu ba.

"Za mu gurfanar da su a kotu. Za mu tuhumesu da laifin haddasa hayaniya, hana zaman lafiya da sauransu."

Dubban matasa ne suka fito zanga-zangar lumana a garin Katsina inda suke bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamna Aminu Bello Masari da su yi murabus.

KU KARANTA KUMA: Zargin Malamin addini da fyade: Kotu ta yi watsi da karar

Sun nuna damuwarsu a kan yadda rashin tsaro ke hauhawa a fadin jihar, yankin arewa maso yamma da Najeriya baki daya.

Matasan karkashin inuwar CNG, sun ce gwamnatin tarayya da gwamnonin arewa maso yamma sun gaza shawo kan matsalar 'yan bindiga a yankin.

A baya mun ji cewa bayan zanga-zangar lumanar da matasa suka yi sakamakon rashin tsaro da yayi Kamari a jihar, jami’an ‘yan sanda sun kama shugaban kungiyar Coalition of Northern Groups (CNG), Nastura Ashir Sharif.

Sharif wanda shine shugaban kwamitin amintattu Coalition of Northern Groups (CNG) na hannun hedkwatar ‘yan sanda da ke Abuja, jaridar Tribune Online ta ruwaito.

A wata takardar da Tribune Online ta samu daga CNG wacce kakakin kungiyar, Abdulazeez Suleiman yasa hannu, ta ce an kama Sharif bayan sun kammala zanga-zangar da suka yi a Katsina a ranar Talata.

Idan zamu tuna, a ranar Talata, dubban matasa daga jihohin arewa karkashin inuwar CNG suka hadu a Katsina inda suka yi zanga-zanga a kan ta'azzar ayyukan ‘yan bindiga a yankin.

Wannan ce babbar zanga-zanga ta farko da ta tattara matasa daga kungiyoyi masu tarin yawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel