Wala-wala a kasuwa ta sa Naira ta yi raga-raga a hannun ‘Yan canji

Wala-wala a kasuwa ta sa Naira ta yi raga-raga a hannun ‘Yan canji

A ranar Laraba, 18 ga watan Yuni, 2020, an saida Dalar Amurka a kan N452 a kasuwar canji a Najeriya. Hakan ya zo ne bayan wasu rade-radi da ke yawo a kasuwar kasar.

Jaridar Punch ta bayyana cewa bashin kasar wajen da ke kan gwamnatin Najeriya ya na cikin abubuwan da su ka yi sanadiyyar karyewar Naira a cikin farkon makon nan.

Babban bankin Najeriya ya dawo da saidawa bankunan kasuwa Dala a cikin watan Afrilu domin masu bukatar biyan kudin makaranta a kasashen waje da kuma shigo da kaya.

Kafin wannan lokaci bankin na CBN ya dakatar da saida Dala ga masu shigo da kaya Najeriya daga ketare. Masu harkar sun shaidawa Jaridar Punch cewa wannan ya kawo matsala.

Shugaban ‘yan kasuwar canji a Najeriya, Alhaji Aminu Gwadabe ya ce dakatar da saidawa bankuna Dala ya jawo matsala a kasuwa, inda rade-radin da ake yi su ka jawo tashin farashi.

KU KARANTA: Lalata da karamar yarinya ya jawowa 'Dan acaba zaman kurkuku

Wala-wala a kasuwa ta sa Naira ta yi raga-raga a hannun ‘Yan canji
Gwamnan CBN Godwin Emefiele
Asali: UGC

Aminu Gwadabe ya ke cewa: “Mutane su na amfani da wannan dama ganin cewa yanzu bashin kudin kasar waje ne hanyar samun kudin shigan Najeriya ba mai ba.”

“Akwai bukatar bankin CBN da kwamitin yaki da annobar cutar COVID-19 su sa ido a kan mugun aikin da ‘yan kasuwar canji su ke yi, domin a ceci kudin Najeriya.”

“Tattalin arzikinmu ya dogara ne sosai da tufafi, mai, abinci, kayan asibti da sauran kaya da ake shigo da su daga kasar waje.” Inji Gwadabe.

Gwadabe ya kuma bayyana cewa akwai bukatar a nemi wasu hanyoyin samun Dala a Najeriya. Daga cikin wadannan hanyoyi akwai aiko kudin kasar waje Najeriya daga ketare.

Shugaban ‘yan canjin ya kara da cewa: “Dala ta koma N452/$ yau (Laraba) a kasuwa, kuma farashin na cigaba da tashi ne, abin na da ban tsoro muddin BDC ba su dawo aiki ba.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel