Yanzu-yanzu: Ajimobi ya rantsar da kwamitin zaben fidda gwani na APC a Edo

Yanzu-yanzu: Ajimobi ya rantsar da kwamitin zaben fidda gwani na APC a Edo

- Jam'iyyar APC mai mulki a ranar Alhamis, ta rantsar da kwamitin zaben gwamnoni na jihar Edo da kuma na daukaka karar zaben fidda gwani da za a yi a ranar 22 ga watan Yuni

- Mukaddashin shugaban jam'iyyar, Abiola Ajimobi ne ya rantsar da shugabannin kwamitin

- Ya umarci kwamitin da su tabbatar da nasara wajen fitar da wanda zai riki tutar jam'iyyar

Jam'iyyar APC mai mulki a ranar Alhamis, ta rantsar da kwamitin zaben gwamnoni na jihar Edo da kuma na daukaka karar zaben fidda gwani da za a yi a ranar 22 ga watan Yuni, don fitar da dan takara a zaben da za a yi a watan Satumba.

Mukaddashin shugaban jam'iyyar na kasa, Sanata Abiola Ajimobi, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa na yankin kudu maso kudu, Hillard Etagbo Eta, ya umarci kwamitin da su tabbatar da nasara wajen fitar da wanda zai riki tutar jam'iyyar.

Kwamitin mutum bakwai ya samu shugabancin Gwamnan jihar Imo, Hope Uzordinma da Sanata Ajibola Bashiru a matsayin sakatare.

Yanzu-yanzu: Ajimobi ya rantsar da kwamitin zaben fidda gwani na APC a Edo
Yanzu-yanzu: Ajimobi ya rantsar da kwamitin zaben fidda gwani na APC a Edo Hoto: Pmnews
Asali: UGC

Kwamitin daukaka karar zaben ya samu shugabancin Dr. Yusuf Nawai da Dr. Kayode Ajulo a matsayin sakatare.

A gefe guda, mun ji cewa darakta Janar din Voice of Nigeria (VON), Osita Okechukwu, ya bayyana dakatar da shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole da kotun daukaka kara tayi a matsayin babban kwanciyar hankali ga jam’iyyar.

Wannan na zuwa ne bayan Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya ce ya amince zai taimaki takwaransa na jihar Edo, Godwin Obaseki, don koyawa Oshiomhole darasi a jihar.

“Na amince zan taimaki Obaseki don koya wa Oshiomhole darasi a jihar Edo. Oshiomhole ya koma ya tambayi Amarchi yadda muka kare,” Wike ya wallafa a shafinsa na Twitter a jiya.

A wata takarda da aka fitar a Abuja, Okechukwu ya ce: “An rabu da kwallon mangwaro, an huta da kuda. Babu shakka Kwamared Adams Oshiomhole bashi da amfani a matsayin shugaban jam’iyyarmu mai albarka.

“An dakatar da shi amma saboda taurin kai ya ki daina ayyukan jam’iyyar don yin biyayya ga kundun tsarin mulkin APC.”

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel