Makomar Obaseki: PDP za ta yi taro a ranar Alhamis

Makomar Obaseki: PDP za ta yi taro a ranar Alhamis

Shugabannin jam'iyyar PDP za su yi taro a ranar Alhamis don tattaunawa a kan makomar gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, wanda ke neman tikitin zarcewa a kujerarsa.

Majiya mai karfi ta ce babbar jam'iyyar adawar ta ce za ta yi taron ne don sauraron rahotanni daga dukkan shugabannin jam'iyyar da gwamnan ya samu ganawa da su a kwanaki biyar da suka gabata.

Obaseki ya gana da Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da Gwamna Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom a ranakun karshen mako kafin ya sanar da fitarsa daga jam'iyyar APC wacce ta hana shi fitowa zaben fidda gwani.

Hakazalika, mataimakinsa, Philip Shaibu ya fice daga jam'iyyar APC tare da sauke tutocinta da ke gidan gwamnati a Benin.

Makomar Obaseki: PDP za ta yi taro a ranar Alhamis
Makomar Obaseki: PDP za ta yi taro a ranar Alhamis Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Obaseki ya samu tattaunawa da shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Uche Secondus da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal.

Yadda jam'iyyar za ta bashi tikitinta na takarar gwamnan jihar Edo ne babban abun tattaunawa a yau, majiya ta tabbatar kuma jaridar The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Me kika taba yi don inganta rayuwar yara- 'Yan Najeriya sun caccaki Aisha Buhari

A wani labarin kuma, mun ji cewa kwamitin gudanar da ayyuka na jam'iyyar APC ya bayyana bukatar maye gurbin mataimakin sakataren jam'iyyar, Victor Giadom da wani.

Hakazalika, 16 daga cikin 'yan kwamitin gudanar da ayyukan jam'iyyar sun amince da Ajimobi a matsayin mukaddashin shugaban jam'iyyar na kasa.

Wadanda basu amince da Ajimobi ba a matsayin mukaddashin shugaban sun hada da mataimakin shugaban jam'iyya na Arewa, Lawal Shuaibu, Giadom da mataimakin shugaban jam'iyya na yankin arewa maso gabas, Mustapha Salihu.

Binciken da jaridar The Nation tayi ta gano cewa NWC sun yanke shawarar kwace kujerar Giadom ganin cewa tun daga 2018 ya daina shugabanci a jam'iyyar.

Giadom ya yi murabus a 2018 saboda tsayawar da zai yi a takarar mataimakin gwamnan jihar Ribas a karkashin jam'iyyar APC.

Amma bayan hana jam'iyyar APC fidda dan takara a 2019, Giadom ya koma ofishinsa da ke hedkwatar jam'iyyar ba tare da anyi sabon zabe ba a yankin kudu-maso kudu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: