Yanzu-yanzu: Sabbin mutane 587 sun kamu da cutar Korona a Najeriya

Yanzu-yanzu: Sabbin mutane 587 sun kamu da cutar Korona a Najeriya

Hukumar hana yaduwar Cututtuka a Najeriya watau NCDC ta sanar da cewa annobar cutar Korona ta sake harbin sabbin mutane 587 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11:18 na daren ranar Laraba, 17 ga watan Yuni na shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 490 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

Lagos-155

Edo-75

FCT-67

Rivers-65

Oyo-56

Delta-50

Bayelsa-25

Plateau-18

Kaduna-18

Enugu-17

Borno-12

Ogun-12

Ondo-7

Kwara-4

Kano-2

Gombe-2

Sokoto-1

Kebbi-1

17,735 sun kamu

5,967 aka sallama

469 sun mutu

Asali: Legit.ng

Online view pixel