Edo 2020: An rufe majalisar jihar Edo na kwanaki 14
An rufe majalisar jihar Edo na tsawon makonni biyu. Mukaddashin daraktar majalisar, Stephen Guobadia ya sanar da hakan a wata takarda inda ya bukaci 'yan majalisar da su kauracewa zauren majalisar har sai an yi mishi feshi.
Wannan ci gaban ya zo ne a yayin da rikici ya rincabe a jam'iyyar APC reshen jihar kafin zuwan zaben fidda gwani da za a yi a ranar 22 ga watan Yunin 2020.
Kwamitin tantancewar jam'iyyar ya hana gwamna Godwin Obaseki tsayawa takara, lamarin da yasa gwamnan ya bar jam'iyyar.
Guobadia ya yi kira ga 'yan jam'iyyar da su kasance suna ayyukansu ta yanar gizo, jaridar The able ta ruwaito.
"An umarceni da in sanar da ku cewa ana bukatar shugabannin majalisar da dukkan ma'aikatanta su zauna a gida na kwanaki 14 daga ranar Talata, 16 ga watan Yunin 2020," takardar ta sanar.
"Wannan ya biyo bayan feshin da za a yi wa ginin majalisar har sau uku.
"Ana shawartar dukkan ma'aikatan majalisar da su kasance da wayoyinsu a koda yaushe koda wani al'amarin gaggawa na iya tasowa."
Ba a rufe zauren majalisar ba duk da kakakin majalisar, Frank Okiye ya harbu da cutar korona a cikin watan Maris.
KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Kogi ta sanar da mutuwar hadimin Gwamna Bello
Okiye ne mutum na farko da ya kamu da cutar a jihar Edo wacce a halin yanzu take da mutum 620 masu cutar. Kakakin ya warke tas bayan kwanaki 21 yana jinya a cibiyar killacewa.
Majalisar jihar Edo din na cikin rudani tun kusan shekarar daya da ta gabata, lamarin da yasa ba a rantsar da mambobi 14 daga cikin 24 tun bayan zabensu.
An samu rabuwar kai tsakanin mambobin inda aka samu wasu na biyayya ga Obaseki ko Oshiomhole.
A wani bayani daban, mun ji cewa Darakta Janar din Voice of Nigeria (VON), Osita Okechukwu, ya kwatanta dakatar da shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole da kotun daukaka kara tayi da babban kwanciyar hankali ga jam’iyyar.
Wannan na zuwa ne bayan Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya ce ya amince zai taimaki takwaransa na jihar Edo, Godwin Obaseki, don koyawa Oshiomhole darasi a jihar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng