Korona: El-Rufa'i ya kaddamar da dakin gwaji na 'tafi da gidanka' a Kaduna (Hotuna)

Korona: El-Rufa'i ya kaddamar da dakin gwaji na 'tafi da gidanka' a Kaduna (Hotuna)

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya kaddamar da cibiyar gwajin cutar korona ta 'tafi da gidanka'.

Cibiyar gwajin, ta zamani, za ta ke zagayawa a sassan birnin Kaduna domin gudanar da gwajin cutar korona a kan mazauna garin.

Kungiyar USAID ta kasar Amurka ce ta aikowa gwamnatin jihar Kaduna tallafin dakin gwajin domin kara mata karfin gwuiwa a kokarinta na ganin an gudanar da gwajin kwayar cutar korona a kan jama'a da yawa.

Hukumar hana yaduwar Cututtuka a Najeriya, watau NCDC, ta sanar da cewa annobar cutar Korona ta sake harbin sabbin mutane 587 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11:18 na daren ranar Laraba, 17 ga watan Yuni na shekarar 2020.

DUBA WANNAN: An kori janar a rundunar sojin Najeriya 'babu girma, babu arziki'

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 490 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

Lagos-155

Edo-75

FCT-67

Rivers-65

Oyo-56

Delta-50

Bayelsa-25

Plateau-18

Kaduna-18

Enugu-17

Borno-12

Ogun-12

Ondo-7

Kwara-4

Kano-2

Gombe-2

Sokoto-1

Kebbi-1

Jimillar mutane 17,735 ne suka kamu da kwayar cutar, an sallami mutane 5,967 daga cibiyoyin killacewa da ke fadin Najeriya, an tabbatar da mutuwa mutane 469 da suka kamu da cutar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng