Edo 2020: APC ta fitar da kwamitin zaben fidda gwani da na daukaka kara (Sunaye)

Edo 2020: APC ta fitar da kwamitin zaben fidda gwani da na daukaka kara (Sunaye)

Kwamitin gudanar da ayyuka (NWC) na jam'iyyar APC a ranar Laraba ya jaddada cewa Sanata Abiola Ajimobi ne mukaddashin shugaban jam'iyyar na kasa, gidan talabijin din Channels ya ruwaito.

Wannan na zuwa ne bayan da kotun daukaka kara ta jaddada dakatar da Kwamared Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam'iyyar kamar yadda sashe na 14.2, sakin layi na uku na kundun tsarin mulkin jam'iyyar ya tanadar.

Mallam Lanre Issa-Onilu, sakataren yada labarai na jam'iyyar APC na kasa ya bayyana wannan ci gaban.

Ya kara da cewa rashin lafiyar Ajimobi yasa NWC suka nada mataimakin shugaban jam'iyyyar na yankin Kudu-kudu, Prince Hilliard Etta yayi aiki a madadin Ajimobi.

Kamar yadda mai magana da yawun APC ya sanar, wannan nadin da suka yi ya samu goyon bayan kundun tsarin mulkin jam'iyyar inda ya jaddada cewa dole mukaddashin ya kasance daga yankin shugaban jam'iyyar na kasa.

Hakazalika, an tsara tare da fitar da sunayen 'yan kwamitin zaben fidda gwani da na daukaka karar zaben fidda gwanin da za a yi a ranar 22 ga watan Yunin 2020.

Wadanda aka zaba sun hada da:

Kwamitin zaben fidda gwani

1. Gwamnan jihar Imo Sanata Hope Uzodinma – Shugaba

2. Sanata Ajibola Bashiru – Sakatare

3. Alh. Abdullahi Abass

4. Hon. Ibrahim Sabo

5. Hon. Ocho Obioma

6. Hajia Amina Lantana Muhammed

7. Hon. Gbenga Elegbeleye

Sunaye: APC ta fitar da kwamitin zaben fidda gwani da na daukaka kara
Sunaye: APC ta fitar da kwamitin zaben fidda gwani da na daukaka kara. Hoto daga Channels TV
Asali: Twitter

KU KARANTA: Buhari ya nada sabbin sakatarorin dindindin 12 (Sunaye da jihohi)

Kwamitin daukaka karar zaben fidda gwani

1. Prof. Mustapha Bello – Shugaba

2. Dr. Kayode Ajulo – Sakatare

3. Hon. Umar Ahmed

4. Nasiru Ibrahim Junju

5. Hon. Rasaq Mahmud Bamu

Jam'iyyar ta kara da kiyaye cewa, hukuncin babbar kotun tarayya da ta yanke ya bayyana Igo Aguma a matsayin mukaddashin shugaban jam'iyyar na jihar Ribas.

Don kiyayewa tare da biyayya ga hukuncin kotun, jam'iyyar ta rungumi Aguma a matsayin mukaddashin shugaban jam'iyyar na jihar Ribas kafin ta yi sabon taro tare da zabar shugabannin jam'iyya a matakin gunduma, karamar hukuma da jiha.

Mambobin kwamitin NWC goma sha shida ne suka halarci taron jam'iyyar da aka yi a babban ofishinta da ke Abuja. Goma sha uku sun halarta da kansu amma uku sun halarta ta yanar gizo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel