Tsaro: Amurka ta aikowa gwamnatin Buhari muhimmin sako

Tsaro: Amurka ta aikowa gwamnatin Buhari muhimmin sako

Gwamnatin kasar Amurka ta yi Alla - wadai da yawaitar kisan fararen hula a Najeriya, musamman a cikin 'yan makonnin baya bayan nan.

A cikin wani jawabi da sakataren gwamnati, Michael Pompeo, ya fitar ranar Laraba, gwamnatin kasar Amurka ta ja hankalin gwamnati a kan kisan fararen hula da 'yan bindiga da mayakan kungiyar Boko Haram ke yi a jihohin Katsina da Borno.

"Mun yi Alla - wadai da wadannan kashe - kashe marasa dalili da babu wata manufa a cikinsu.

"A 'yan makonnin baya bayan nan, mayakan kungiyar ISIS a yankin Afrika ta yamma sun kai hare - hare tare da kashe fararen hula fiye da 120; da suka hada da mata da kananan yara, a jihar Borno.

"A ranar 9 ga watan Yuni, wasu 'yan bindiga sun kai hari wani kauye a Katsina tare da kashen dumbin mutane.

"Wadannan kashe - kashe sun biyo bayan harbe wani Fasto da matarsa mai juna biyu a ranar 1 ga watan Yuni da kisan wani Limami, Dagachi, da dumbin fararen hula a ranar 5 ga watan Yuni a wani rikicin kabilanci da ya barke a jihar Taraba," a cewar Pampeo.

Gwamnatin kasar Amurka ta bukaci gwamnatin Najeriya ta kara kokarinta na kare rayukan jama'a ta hanyar kawo karshen aiyukan ta'addanci tare da hukunta 'yan ta'adda.

Tsaro: Amurka ta aikowa gwamnatin Buhari muhimmin sako
Buhari da jakadan Amurka a Najeriya
Asali: Facebook

"Dubun dubatar jama'a sun rasa rayukansu a Najeriya a 'yan shekarun baya bayan nan sakamakon munanan hare - haren da kungiyoyin 'yan ta'adda ke kaiwa, yayin rigingimun kabilanci, ko kuma rigingimu masu nasaba da addini," a cewar sakataren gwanatin Amurka.

DUBA WANNAN: Shekau ya saki sabon bidiyo, ya nemi 'yan bindiga su hada kai da Boko Haram

Pampeo ya kara da cewa"Kasar Amurka ta na kira ga gwamnatin Najeriya a kan ta kara karfafa kokarinta na kawo karshen rashin zaman lafiya, a hukunta masu laifi, a kare rayukan fararen hula."

Jaridar HumAngle ta rawaito cewa kimanin 'yan Najeriya 261 ne suka rasa rayukansu, musamman a yankin arewa, daga ranar Litinin, 8 ga watan Yuni, 2020, zuwa ranar Asabar, 13 ga watan Yuni, 2020.

Hakan na nufin an samu karuwar kaso 32% a kan adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon hare - haren 'yan bindiga a cikin satin farko na wata Yuni.

A jawabin ranar dimokradiyya da ya gabatar, shugaba Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta bayar da fifiko wajen yaki da 'yan ta'adda.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa an kwace dukkan kananan hukumomi da mayakan kungiyar Boko Hara suka kwace iko da su a jihohin Adamawa, Borno da Yobe, duk da bayanai sun nuna sabanin hakan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng