Korona: Bincike ya nuna jinjiri da ke ciki baya harbuwa da cutar daga mahaifiya

Korona: Bincike ya nuna jinjiri da ke ciki baya harbuwa da cutar daga mahaifiya

Sabon bincike da aka yi a jami'ar Nottingham da ke Ingila ta bayyana cewa jinjiri baya iya daukar cutar coronavirus daga mahaifiyarsa yayin da yake cikinta.

Wata mujallar duniya da ta shafi cututtukan mata, ta ce samun cutar bai da wani tasiri sosai idan an haifi jinjirin ta gaba, aka, shayar da shi, kuma aka bari ya yi tarayya da mahaifiyar.

Masu binciken sun gano cewa kananan alamun cutar ake samu marasa tasiri a jikin jariran da suka kamu da cutar.

Amma kuma sunce hujjoji kadan ne ke iya tasiri a kan hakan.

COVID-19: Bincike ya nuna jinjiri da ke ciki baya harbuwa da korona daga mahaifiya
COVID-19: Bincike ya nuna jinjiri da ke ciki baya harbuwa da korona daga mahaifiya Hoto: Premium Times
Asali: UGC

A binciken da suka gudanar, mata 655 masu cutar korona sun haifa jarirai 666 saboda wasu tagwaye suka haifa.

Daga cikin matan da suka haihu da kansu, takwas cikin 292 (kaso 2.7) ne kadai jariransu suka kamu da korona.

Daga cikin mata 365 da aka yi wa tiyata kuma, 20 (kaso 5.3) ne kadai yaransu suka kamu da OVID-19.

Kamar yadda masu binciken suka tabbatar jariran basu nuna wata alamar harbuwa da cutar ko bayan kamuwarsu.

Daya daga cikin masu binciken kuma farfesa a jami'ar Nottingham, Dr Kate Walker, ta ce, "hankula sun tashi a kan yuwuwar mai ciki ta shafa wa jinjiri cutar coronavirus.

"Mun so mu gane ta inda iyayen suka shafa wa jariran. Ta shayarwa ne ko kuma wurin haihuwa.

"Daga bincikenmu mun gano cewa yuwuwar kamuwar jarirai kadan ce. Za mu kara jaddada cewa shayar da su tare da haihuwarsu da kai babu wata matsala a ciki.“

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Kogi ta sanar da mutuwar hadimin Gwamna Bello

Hakazalika da take magana wata likita a jami’ar Dalhousie, Dr. Jeannette Comeau, ta ce: “nayi farin ciki da ganin cewa alkaluman na ci gaba da tabbatar da ajiye uwa da jinjiri a tare bayan haihuwa.

“Daga lamarin kamuwar jarirai sabbin haihuwa, bamu da tabbataccen hujjar cewa an samu wannan cuta ne a mahaifa ko kuma a lokacin haihuwa.”

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel