Bayan kashe-kashe da zanga-zanga, IGP, NSA, da shugaban DSS, shugaba NIA sun dira Katsina

Bayan kashe-kashe da zanga-zanga, IGP, NSA, da shugaban DSS, shugaba NIA sun dira Katsina

Bayan kwanaki ana zanga-zanga sakamakon kashe-kashen mutane a jihar Katsina, Sifeto Janar na hukumar yan sanda, IG Mohammed Adamu, ya dira jihar tare da manyan jami'an gwamnatin Buhari.

Daga cikin wadanda ke cikin tawagar sune Dirakta Janar na hukumar DSS, Yusuf Magaji Bichi; mai bada shawara kan lamuran tsaro, Babagana Monguno; shugaban hukumar leken asirin kasa NIA, da sauran manyan jami'an yan sanda.

Daga dirarsu babban tashar jiragen sama, Umaru Musa Yar'adua, IGP na manyan jami'an sun garzaya gidan gwamnatin jihar domin ganawa da gwamnan Aminu Bello Masari.

Hadimin Buhari kan sabbin kafafen yada labarai ya bayyana cewa manyan jami'an tsaron sun je Katsina ne domin shira rundunar hadin kai tsakanin Soji da yan sanda kan yadda za'a kawar da yan ta'adda a Katsina, Kaduna, Neja, Zamfara da Sokoto.

Bayan kashe-kashe da zanga-zanga, IGP, NSA, da shugaban DSS sun dira Katsina
IGP, NSA, da shugaban DSS sun dira Katsina
Asali: UGC

Ku dakaci cikakken rahoton....

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel