NCDC ta yi magana kan shan Dexamethasone wajen warkar da COVID-19

NCDC ta yi magana kan shan Dexamethasone wajen warkar da COVID-19

- Wasu Masana a Jami’ar Oxford sun samu nasara a binciken Coronavirus

- Ana sa rai an samu maganin da zai iya rage karfin kwayar cutar COVID-19

- NCDC ta ce a dakata da amfani da Dexamethasone har sai WHO ta amince

Masu bincike da nazari game da annobar COVID-19 a jami’ar Oxford ta kasar Birtaniya, sun yi nisa a aikin da su ke yi na samo kwayar maganin da zai warkar da cutar.

BBC ta bayyana cewa wadannan masana sun ce kwayar Dexamethasone zai iya aiki wajen warkar da wadanda su ka kamu da cutar Corornavirus.

Wani abin farin ciki shi ne wannan magani da ake tunani zai yi wa masu COVID-19 aiki ya na da araha kwarai da gaske, sannan ya na da saukin samu a kasuwa.

A cewar BBC, maganin zai ceci kashi daya cikin uku na marasa lafiyan da ke numfashi ta na’ura.

Wannan magani na Dexamethasone zai ceci kashi daya cikin biyar na masu jinyar Coronavirus da su ke numfashi ta iskar bature na asibiti.

KU KARANTA: Masu dauke da COVID-19 su na cigaba da kara yawa a Najeriya

NCDC ta yi magana kan shan Dexamethasone wajen warkar da COVID-19
Firayim Ministan Ingila, Boris Johnson
Asali: Twitter

Da ace an yi amfani da wannan magani tun farkon lokacin da annobar COVID-19 ta barke a Ingila, da yanzu mutane akalla 5, 000 ba su mutu ba.

Dama can ana amfani da kwayan Dexamethasone wajen maganin kumburin jiki da cutar numfashi da kuma ciwon gabbai da tsofaffi kan yi fama da shi.

Masana kiwon lafiya sun ce Dexamethasone zai taimaka sosai wajen taimakawa garkuwar jiki a lokacin da ta ke yaki da kwayar cutar Coronavirus.

Wannan ya sa gwamnatin Birtaniya ta tanadi kwalaye 200, 000 na wannan magani ta boye domin a rika ba masu cutar a asibiti. Gwamnatin Najeriya ta ce ka da a fara amfani dashi tukuna.

A lokacin da kasar Ingila ta ke murna da wannan cigaba da aka samu, hukumar NCDC ta ce ta san da labarin wannan bincike, amma a jira sai WHO ta yarda a rika ba masu jinya wannan magani.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng