Iyakar Zamfara da Katsina: Dakarun sojin sama sun ragargaza sansanin 'yan ta'adda

Iyakar Zamfara da Katsina: Dakarun sojin sama sun ragargaza sansanin 'yan ta'adda

Hedkwatar tsaro ta kasa ta ce rundunar Operation Hadarin Daji ta ragargaza sansanin 'yan bindiga tare da halaka wasu har lahira a dajin Katsina da ke kudancin Birnin Kogo kusa da iyakar Katsina da Zamfara.

Shugaban fannin yada labarai na rundunar sojin Najeriya, John Enenche, a wata takarda da ya fitar a Abuja, ya ce samamen da suka kai ci gaba ne na kawo karshen ta'addanci a yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya a kasar nan.

Enenche ya ce an aiwatar da harin ta jiragen yaki ne a ranar Litinin karkashin wani sashi na atisayen Operation Accord bayan bayanan sirri da dakarun suka samu na maboyar 'yan ta'addan.

Ya yi bayanin cewa, bayanan sun nuna tabbaci a kan maboyar 'yan bindigar na nan inda wasu bukkoki suke. Suna amfani da wurin a matsayin karamin sansani wanda shahararren dan bindiga "Adamu Aleiro" ke jagoranta.

Kamar yadda yace, dakarun sojin saman sun tura wasu jami'ai inda suka kai hari da jiragen yaki, hakan yasa aka tarwatsa sansani uku a yankin.

Iyakar Zamfara da Katsina: Dakarun sojin sama sun ragargaza sansanin 'yan ta'adda
Iyakar Zamfara da Katsina: Dakarun sojin sama sun ragargaza sansanin 'yan ta'adda. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Harin 'yan bindiga: Jama'a ta za su kare kansu idan FG ba za ta iya ba - Sanata

"An kashe 'yan ta'adda masu tarin yawa a harin.

"Shugaban rundunar sojin saman, Air Marshall Sadique Abubakar, ya jinjinawa rundunar Operation Hadarin Daji a kan kwarewarsu da suka nuna.

"Ya yi kira garesu da su ci gaba da ayyukan da suke don kawo karshen ta'addanci a yankin.

"Hakan ne zai sa mu cimma umarnin shugaban rundunar tsaro ta kasa na dawo da zaman lafiya a jihohin yankunan arewa maso yamma da ta tsakiya a fadin kasar nan," yace.

A wani labari na daban, kungiyoyi masu zaman kansu a jihar Katsina za su fito zanga-zangar lumana a fadin jihar a ranar Talata don nuna fushinsu ga gwamnatin tarayya da ta jihar sakamakon kashe-kashen da yayi yawa a jihar.

Kwamared Yasin Ibrahim, shugaban kungiyar, ya sanar da jaridar HumAngle a ranar Litinin da dare "Mun shirya yin zanga-zangar Lumana a gobe don nuna bacin ranmu ga hukumomi.

"Mun gano cewa gwamnati bata shirya kawo karshen kashe-kashe, salwantar dukiyoyi da fyade da ake yi wa matanmu, iyayenmu da kannanmu ba.

"Wannan zanga-zangar bata da alaka da siyasa, sako ne mai sauki. Shugaban kasa muke bukatar ya zo ya yi mana gyaran fannin tsaro."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel