Rashin Tsaro: An yi zanga-zangar neman Buhari da Masari su yi murabus
A ranar Talatar da ta gabata masu zanga-zanga suka mamaye fadar gwamnatin jihar Katsina, suna neman shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Aminu Masari su yi murabus.
Matasa sun yi zanga-zangar ne domin nuna damuwa dangane da yadda matsalar tsaro ke ci gaba da tabarbarewa a jihar da ke Arewa maso Yammacin kasar nan.
A ranar 9 ga watan Yuni, 'yan daban daji suka fantsama jihar, inda suka kashe kimanin mutane 40 tare da yin garkuwa da wasu matasa da kananan yara da dama.
An kuma ruwaito cewa, maharan sun yi ma mata da dama fyade sa'annan kuma sun kashe dabbobi masu yawa.
Damuwa da lamarin, ya sa matasa a birnin Dikko, suka kai ziyarar ba zata har fadar gwamnatin jihar, inda suka rika kukan Buhari da Masari su yi murabus tun da dai ba zasu iya tsare musu rayukansu ba.
Su na waƙen "a kawo karshen 'yan daban daji," "ya isa haka." "Tura ta kai bango." "Jihar Katsina gidan kara ne da saukar baƙi." "Zaman lafiya kawai muke so."
Matasan sun yi ta rera wakokin nuna adawa da gwamnati, suna kira da a dauki matakin gaggawa don kawo kashe-kashen da ake yi a jihar.
Wasunsu sun zargi gwamnati da bayar da uzuri masu yawa kuma masu rauni, suna kira da gwamna Masari ya yi murabus cikin gaggawa.
KARANTA KUMA: Covid-19: Mun samu gudunmuwar N1.69bn tsakanin watan Afrilu da Mayu - Gwamnatin Tarayya
Ana iya tuna cewa, Gwamna Masari yayi martani dangane da kisan mutum 40 da aka yi kwanan nan a jihar, ya yarda da gazawarsa a matsayin gwamnan da ya kasa tsare rayukan al'umma.
Legit.ng ta ruwaito cewa, Shugaba Buhari, ya roki mutanen Katsina su kara hakuri tare da bawa gwamnatinsa hadin kai da goyon baya a kokarinta na tabbatar da an samu zaman lafiya a jihar.
Buhari ya bayyana hakan ne a cikin wani jawabi da kakakinsa, Garba Shehu, ya fitar a ranar Talata.
A cikin jawabin, shugaba Buhari ya mika sakon ta'aziyya da jaje ga wadanda suka yi asarar makusanta da dukiya sakamakon hare-haren 'yan bindiga.
A cewar shugaba Buhari, rundunonin tsaro na kasa za su iya shawo kan kalubalen tsaron da 'yan bindiga da 'yan ta'adda suka jefa kasa a ciki.
Shugaba Buhari ya yi gargadin cewa mamaye tituna da sunan zanga - zanga zai iya kawo tsaiko ga aikin rundunar soji na murkushe 'yan bindiga a jihar Katsina.
Kazalika, ya yi kira ga mutanen jihar Katsina da su bawa sojoji hadin kai domin za su kawo karshen 'yan ta'adda da aiyukan ta'addanci a cikin kankanin lokaci.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng