Za mu kori Likitocin da su ka ki zuwa wurin aiki a Ranar Laraba – Inji Enahire

Za mu kori Likitocin da su ka ki zuwa wurin aiki a Ranar Laraba – Inji Enahire

Gwamnatin tarayya ta yi barazanar sallamar likitocinta daga aiki muddin ba su yi watsi da maganar zuwa yajin-aiki, su ka koma asibitoci domin su cigaba da kula da marasa lafiya ba.

Jaridar Vanguard ta ce gwamnatin Najeriya ta bukaci likitoci su koma aiki a yau Laraba, inda ta ce za ayi bincike kuma a hukunta duk wanda aka samu bai hallara a asibiti a yau ba.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnati ta bukaci shugabannin asibitoci su rika ajiye littafin da za a rika sa hannu a duk lokacin da aka shiga ofis domin a tabbatar da masu zuwa aiki.

Wannan barazana ta fito ne daga bakin ministan harkar lafiya na kasa, Osagie Ehanire, bayan an gaza samun matsaya a zaman tattaunawar da su ka yi da kungiyar manyan likitocin.

Kungiyar NARD ta masu shirin zama kwararrun likitoci a Najeriya sun shiga yajin aikine a ranar Litinin. Har yanzu dai ministan harkar kiwon lafiyan ya gaza shawo kan likitocin kasar.

A zaman da aka yi jiya Talata wanda aka fara da kimanin karfe 1:00, an tashi baram-baram babu matsaya tsakanin bangarorin inda shugaban NARD, Aliyu Socumba, ya fice a fusace.

KU KARANTA: Buhari ya raba sababbin mukamai a ma'aikatar gwamnatin tarayya

Za mu kori Likitocin da su ka ki zuwa wurin aiki a Ranar Laraba – Inji Enahire
Ministan harkar lafiya na kasa, Osagie Ehanire Hoto: Business Day
Asali: Facebook

Dr. Aliyu Socumba ya ke cewa: “Ba za mu dawo aiki ba, mun fada masu cewa za mu iya janye yaji nan da sa’a 24 idan aka yi wani hobbasa, amma a yanzu dai yajin aiki na nan.”

Shugaban kungiyar ta NARD ya kara da cewa: “Ni dai ba zan dawo ba, wasu za su iya dawowa. Matsayarmu shi ne ba a cinma bukatunmu ba…ta yadda za a samu yarjejeniya.”

“Mun fadawa ministan kwadago da samar da aikin yi cewa da zarar mun cin ma wata matsaya mai karfi, za mu kira zama da su a cikin sa’a 24 domin mu sake duba batun yajin.”

Minista Dr. Osagie Ehanire wanda watakila bai ji dadin yadda shugabannin kungiyar likitocin su ka fice daga wurin taron ba, ya ce za a rika daukar sunayen masu zuwa aiki a asibiti.

Da ya ke magana da manema labarai Ehanire ya ce kungiyar ta nuna masu tarurin-kai, amma ya ce za su dauki matakin gaggawa domin ba za a bar asibitoci a yanzu babu likitoci ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel