NBET: Amobi ta cigaba da aiki duk da Ministan wuta ya umarci ta fita daga ofis

NBET: Amobi ta cigaba da aiki duk da Ministan wuta ya umarci ta fita daga ofis

Babbar Darektar NBET ta kasa, Marilyn Amobi, ta cigaba da aiki a ofishinta, duk da cewa kuwa Ministar harkar wutar lantarki, Injiniya Saleh Mamman ya ba ta umarni ta sauka daga kujerarta.

Jaridar Punch ta fitar da rahoto jiya cewa har a ranar Talata, Misis Marilyn Amobi ta yi aiki a ofis. Hakan na zuwa ne bayan Ministan wuta ya fatattake ta daga matsayin da ta ke kai a farkon makon nan.

Mamman ya bada sanarwar cewa Marilyn Amobi za ta tafi hutu, inda Nnaemeka Eweluka zai hau kujerarta. Wannan ne karo na biyu da Mai girma Ministan ya kori shugabar NBTE, amma ta na dawowa aiki.

A 2019, an yi irin haka a lokacin da Ministan wuta ya tsige Marilyn Amobi. Nan take gwamnatin tarayya ta cire NBTE daga karkashin kulawar ma’aikatar wuta, ta maidata karkashin ma’aikatar kudi.

KU KARANTA: 'Yan Majalisa su na so a binciki kamfanin saida wutan Najeriya

NBET: Amobi ta cigaba da aiki duk da Ministan wuta ya umarci ta fita daga ofis
Ministan wuta Saleh Mamman
Asali: Facebook

Bayan Ministan ya bada sanarwar tsige Amobi, sai kuma wata takarda ta fito daga ma’aikatar kudi inda sakataren din-din-din na ma’aikatar, Mahmoud Isa-Dutse, ya ce Amobi za ta cigaba da aikinta.

Mahmoud Isa-Dutse ta bakin ministar kudi ya ce babbar darektar ta kamfanin NBTE ta kasa za ta bar mukamin ta ne a lokacin da wa’adinta zai cika a Ranar 24 ga watan Yulin 2020.

Jaridar ta ce Amobi ta zabi ta cigaba da aiki ne duk da matakin da Saleh Mamman ya dauka bayan ta samu wannan wasika daga ma’aikatar kudi.

Jami’an kamfanin gwamnatin sun tabbatarwa ‘yan jarida cewa har a jiya Amobi ba ta sauka daga kujerarta ba, ta mika ragamar aiki ga Eweluka kamar yadda aka bukace ta ba.

Rahoton da mu ke samu a yanzu shi ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo da kamfanin a karkashin ma’aikatar lantarki, ganin cewa babu abin da ya hada shi da ma’aikatar tattalin arziki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel