Oshiomhole na tsoron masu ilimi, saboda bashi da shi - Obaseki

Oshiomhole na tsoron masu ilimi, saboda bashi da shi - Obaseki

Gwamna Obaseki na jihar Edo ya ce Adams Oshiomhole, shugaban jam'iyyar APC na tsoron masu ilimi saboda 'bai je makaranta' ba.

A yayin zantawa da manema labaran gidan gwamnati a ranar Talata, Obaseki ya zargi Oshionmhole da bakin ciki, kamar yadda jaridar The Cable ta wallafa.

Gwamnan wanda ke fama da rikici da Oshiomhole, an hana shi takarar gwamnan jihar Edo karkashin jam'iyyar APC.

Da aka tambayesa ko zai bada damar yin zaben fidda gwanin a jihrsa, Obaseki ya ce: "Oshiomhole bai bada damar a yi zaben a jihar ba da kuma dakatarwar ba, meye amfanin yi a jihar yanzu?

"Kana tsoron jama'a masu ilimi saboda baka je makaranta ba. Kana tsoron jama'ar da ke da abinda za su iya yi saboda baka san komai ba da ya wuce fada da rikici."

A zargin rashin daidaito game da shaidar takardunsa na karatu, gwamnan wanda ya kwatanta Oshiomhole da mutum mara dabi'a da adalci, ya ce shugaban jam'iyyar APC ya yi amfani da wannan damar ne kawai don cimma manufarsa.

Ya zargi jam'iyyar APC da bai wa Oshiomhole karfin ikon da babu irinsa, hakan kuwa zai saka jam'iyyar mai mulkin cikin hadari.

Oshiomhole na tsoron masu ilimi, saboda bashi da shi - Obaseki
Oshiomhole na tsoron masu ilimi, saboda bashi da shi - Obaseki. Hoto daga The Cable
Asali: UGC

KU KARANTA: Zamfara: Matashi ya yi wa matar yayansa fyade daga bisani ya kasheta

"Babu rashin daidaituwa a takarduna. Matsalar ta fara a 2016 lokacin da na yi takarar gwamnan jihar sai ban ga takardun makaranta na ba saboda ajiyar da nayi musu.

"Daga nan sai na je kotu na karbo shaida wacce na yi amfani da ita. Daga baya na samu takardun kuma a halin yanzu suna tare da ni. Don haka ban san wani rashin daidaito ba.

"Ta yuwu rashin daidaituwar na takardar shaidar kammala hidimar kasana inda yace babu harafi daya a cikin sunan mahaifina. Amma ba hakan bane, salon rubutu ne kawai.

"Don haka ni ban san wani rashin daidaito ba. Wannan abun takaici ne yadda mutane masu irin wannan halin suke shugabantar jam'iyya mai mulki.

"A garesa, neman hanyar yanke hukuncin da yaso ne kuma abun takaici ne yadda tsarin jam'iyyar a yau ya bashi dama. Wannan yana da matukar hatsari.

"Idan ka bai wa wani karfin iko da kuma nauyi jagorancin mutane amma bashi da dabi'a da adalci, dole ne a samu babbar matsala daga baya," yace.

Gwamnan ya bayyana tabbacin cewa zai ci zaben ranar 19 ga watan Satumba tunda jama'a na sonsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel